Posts

Showing posts from 2024

Malam magana ake ta matasa a yau lokaci yayi dole mufito muba mara da kunya

 Malam magana ake ta matasa a yau lokaci yayi dole mufito muba mara da kunya 

Halin da makarantar firamare ta garin Bargi ke ciki a karamar hukumar Kiru.

Image
Halin da makarantar firamare ta garin Bargi ke ciki a karamar hukumar Kiru. Shekaru biyu bayan rahoton Premier Radio kan mummunan halin da makaranta ke ciki har yanzu ba abinda ya sauya.  

DA DUMI-DUMI: EFCC ta dakatar da amfani da Dala, ta umurni Ofisoshin Jakadanci su koma ƙarbar Naira

Image
  DA DUMI-DUMI: EFCC ta dakatar da amfani da Dala, ta umurni Ofisoshin Jakadanci su koma ƙarbar Naira Hukumar EFCC ta umurci ma’aikatan kasashen waje da ke Najeriya da ofisoshin Jakadanci, su daina mu’amala da kudaden waje, su koma yin amfani da Naira wajen gudanar da harkokinsu na hada-hadar kudi,  A Yau ta ruwaito EFCC ta kuma umarci ma’aikatan Najeriya da ke kasashen waje da su karbi Naira a kasuwancinsu na kudi. Hukumar ta ce ta dauki matakin ne domin magance matsalar dala a tattalin arzikin Najeriya da kuma tabarbarewar darajar Naira. LIKE // SHARE & FOLLOW US >

Kamfanoni ne ya kamata su biya harajin tsaron intanet ba mutane ba

Image
  ASALIN HOTO Dama tun tuni akwai dokar tattara harajin tsaro ta intanet a Najeriya, yanzu ne kawai aka fara neman aiwatar da ita, wadannan sune kalaman masanin tattalin arziki Aliyu Da'u Aliyu. Ya bayyana hakan ne a cikin shirin Ra'ayi Riga na BBC Hausa da ake gabatarwa a kowacce Juma'ar ƙarshen mako. Shirin wanda ya samun bakuncin Sanata Shehu Umar Buba wanda ya gabatar da kudurin a gaban majalisar dattijan Najeriya da Honarabil Ali Madakin Gini dan Majalisar wakilan Najeriya da Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Consulting kuma masani kan harkokin tsaro da Malam Adam Hassan shugaban kungiyar 'yan tireda na arewacin Najeriya. Yayin tattaunawar da aka yi Aliyu Da'u Aliyu ya ce a mahangarsu ta tattalin arziki babu bukatar ƙara ƙaƙabawa dan Najeriya ƙarin haraji a yanzu, musamman idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a ƙasar. Shi kuwa Honarabil Ali Madakingini cewa ya yi, dokar ba ta shafi daidaikun mutane ba. "Ta taƙaita ne kan kamfanonin sadar

Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Katsina

Image
 ‘Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Katsina Rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun yi nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Faskari da Malumfashi a jihar, a ranakun 8 da 9 ga watan Mayun 2024. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce ‘yan bindigar sun kai harin farko ne a ranar 8 ga watan Mayu, 2024, bayan sun tare hanyar Funtua zuwa Gusau, a kauyen Unguwar Boka, a karamar hukumar Faskari. A cewarsa, ‘yan ta’ad-dan sun far wa fasinjojin da ke tafiya a cikin wata kirar motar Golf III, inda suka ci da halbe-halbe. Sai dai Sadiq ya bayyana cewa shirin nasu ya ci tura sakamakon wani dauki da jami’an sintiri suka kai. Daily news hausa

WATA SABUWA: Tallafin man fetur da Tinubu ya dawo da shi zai kwashe kusan rabin kudin man fetur da Najeriya za ta sayar – inji IMF

Image
 WATA SABUWA: Tallafin man fetur da Tinubu ya dawo da shi zai kwashe kusan rabin kudin man fetur da Najeriya za ta sayar – inji IMF Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF ya yi gargaɗin cewa maido da tallafin man fetur da Najeriya ta yi zai laƙume kusan rabin kudaden shigarta na man fetur a bana, wanda hakan zai hana Gwamnati samun damar aiwatar da ayyukan da ta tsara za ta yi a bana, A cewar IMF tallafin zai janyo wa Najeriya hasarar kudin danyen mai na kusan fiye da dala tiriliyan 8.43 (dala biliyan 5.9) daga cikin kudin da ƙasar ta yi hasashen za ta samu na naira tiriliyan 17.7 na kudin man fetur, in ji IMF a wani rahoto da ta fitar... Daga shafin, A Yau

Chelsea za ta yi nazari,kan makomar Pochettino, Flick zai koma Bayern Munich

Image
  GETTY IMAGES Bayanan hoto, Mauricio Pochettino Chelsea  za ta yi nazarin karshen kakar wasa ta bana bayan wasan karshe na gasar Premier da za ta yi da  Bournemouth , inda za ta yanke shawara kan makomar kocinta Mauricio Pochettino.  (Telegraph) Arsenal  na zawarcin tsohon mai tsaron ragar kungiyar da Poland Wojciech Szczesny, mai shekara 34, da golan Brighton Jason Steele dan Birtaniya da kuma na Ajax Diant Ramaj dan kasar Jamus yayin da su ke neman wanda zai maye gurbin Aaron Ramsdale, mai shekara 25 wanda zai bar Gunners.  (Standard) Har illa yau  Arsenal  na kuma duba yiwuwar daukar golan  Everton  da Ingila Jordan Pickford, mai shekara 30 a wannan bazara.  (Teamtalk) Gunners  na kuma neman dan wasan baya da tsakiya da kuma mai kai hari a kokarin da suke yi domin fadada 'yan wasan kungiyar karkashin jagorancin Mikel Arteta.  (Standard) Graham Potter ya ki amincewa da damar da aka bashi na zama kociyan Ajax, bayan da ya kasance wanda ke kan gaba a matsayin jagoran kungiyar ta N

#innalillahi... Abun yanamin ciwo araina inajin ba dadi. Idan na kalli rayuwata

Image
 #innalillahi... Abun yanamin ciwo araina inajin ba dadi. Idan na kalli rayuwata  Duniya tayi zafi rayuwa Tana neman yin juyin juya Hali..  Ilimi yazama tarihi a unguwanin mu..  Shin menene matsalar NE  A iya fahimtata masu kudin mu Da shuwagabanin mu sune basa kaunar ganiin muncigaba a Harkar ilimi  Sceince sunyi gsky dasuke cewa marabar Dan adam Da dabba shine tunani,hankali, dakuma kwakwalwa Da aikinta..  Ayau anwayi gari ana amfanin Da jahilicin mu wajen maidamu dabbobin kwantarwa ayanka  Ina ganin hakkin mutunne matukar yanada dabba yaciyar Da ita halak Mufa mutanene babu Wanda zai ciyar damu sai Allah.. Toh meyasa Ta karfi dayaji saikun maidamu dabbobi ta hanyar nesantamu Da ilimi   Rayuwar karatun talaka Da dayanxu  Before jamb 2500 but yanzu 5k  Before neco 25k yanzu Kuma 35k Before WA. Ec 30k yanxu 40k  Ana siyasantar mana Da ilimi haba  Yabaxamu jii ba dadiba  Wlh karkuyi tunanin muka Bari suka rabamu Da ilimi toh wann abubuwan su zasu karu  Yunwa zata yawaita  Tsanani zai ts

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya biya wa daukacin maniyyata aikin bana daga jihar kudin hadaya.

Image
 Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya biya wa daukacin maniyyata aikin bana daga jihar kudin hadaya. Kudin hadayar kowane Alhaji dai sun kama Riyale 720 kwatankwacin Naira 280,000

Sabon filin jirgin saman Dubai da za a kashe Dala bilyan 35 wajen gina shi

Image
  Sabon filin jirgin saman Dubai da za a kashe Dala bilyan 35 wajen gina shi, da za a kammala aikin rukunin farko a shekaru 10. DW Hausa

Babban Zauren MDD ya nemi Kwamitin Sulhu ya amince da ƙasar Falasɗinu

Image
  Copyright: Reuters BABAN zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi ƙira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar da ya tabbatar da 'yancin Falasɗinawa ta hanyar amincewa da kasar a matsayin mamba a majalisar. Falasɗinu dai na da matsayin ƙasa 'yar sa ido tun shekarar 2012, wani abu da ke nuna rashin cikakken 'yancinta na kasancewarta ƙasa mai 'yancin a zauren. Kwamitin Tsaro na Majalisar ta Dinkin Duniya ne kawai yake da damar tabbatar da hakan. Amurka za ta hau kujerar naƙi dangane da zaman Falasɗinu samun matsayin zaman cikakkiyar mamba a kwmaitin. To sai dai zaɓen na ranar Juma'a ya nuna irin goyon bayan da ake nuna wa ƙasar Falasɗinawa. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Turai ke ƙoƙarin amincewa da ƙasar Falaɗinawa.

Dalilin mu na maka gwamnonin Najeriya a kotu- SERAP

Image
  ASALIN HOTON, GOV UBA SANI/FACEBOOK Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta yi ƙarin haske akan dalilan kai ƙarar gwamnonin ƙasar 36 da kuma ministan birnin tarayyar Abuja gaban kotu. Kungiyar ta ce ta shigar da wannan kara ne saboda rashin bayar da bayanai kan yadda gwamnonin jihohin Najeriya 36 da ministan Abuja, suka kashe kuɗaɗen da suka ciyo na bashin naira tiriliyan kusan shida, da kuma sama da dala billiyan 4 da rabi, ba tare da bahasi ba. SERAP ta buƙaci kotun da ta gayyaci hukumar EFCC da ICPC domin ƙaddamar da bincike kan yadda aka kashe basusukan da gwamnonin suka karɓo. Kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta ce ta shigar da karar ne a ranar juma'ar makon da ya gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja. SERAP din ta ce, ta shigar da karar ne bayan gazawar gwamnonin wajen yi wa al'ummar su bayanin yadda suka kashe basusukan da suka karɓo da wajen da aka aiwatar da auikin da aka karbo bashin dominsu. Kolawole Olu

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga a Neja da Borno

Image
  ASALIN HOTO Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakarunta sun samu nasarar kashe 'yan bindiga da dama a jihohin Borno da Neja. Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojin saman ƙasar, Edward Gabkwet ya ce cikin jerin wasu hare-hare ta sama da dakarun rundonin Hadin Kai da Whirl Punch suka ƙaddamar a jihohin biyu ya samu narasar lalata wasu shirye-shiryen 'yan bindigar. Edward Gabkwet ya ce a ranar 3 ga watan Mayu dakarun ƙasar sun kai hari a garin Chinene da ke yankin tsaunin Mandara da ke kusa da jihar Borno. Ya ce dakarun sojin ƙasar sun ga 'yan bindigar na wani taro da ake kyautata zaton tattaunawa suke yi a lokacin da jirgin sojin ya kai musu hari tare da kashe su. “Haka kuma a garin sojojinmu sun hangi wasu motocin yaƙi bakwai da ake zaton na 'yan bindigar ne a ƙarƙashin wata bishiya, nan take su ma aka kai musu hari tare da lalata su'', in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa “bayanan da muka samu bayan hare-haren sun nuna cewa an samu nasara

HOTONAN Yadda Kabilar Dakarkari ke cigaba da gudanar da wasannin al'adun Gargajiya Zuru Uhola.

Image
HOTONAN Yadda Kabilar Dakarkari ke cigaba da gudanar da wasannin al'adun Gargajiya Zuru Uhola. Bikin raya al'adun Gargajiya na kabilar Dakarkari dake masarautar Zuru a jihar kebbi biki ne da ake gudanarwa domin nuna godiya ga Allah. Dubban al'umma ne ciki da wajen jihar suka halarci taron ciki hadda dan majalisar tarayyar Najeriya mai wakiltar masarautar Zuru Hon Kabir Ibrahim Tukura. Hoto📷 Abbakar Aleeyu Anache  

Allah Mai girma

Image
 ALLAH MAI GIRMA : Sama da dalbai dubu biyu ne ke tsare saboda goyon bayan Falasdinawa a kasar Amurka.  Mafiya yawansu ɗalibai ne daga manya jami'o'in kasar Amurka.  Kamar yadda Shashin Turanci na  DW Ingilishi  ta bayyana..

Babu tabbas akan yiyuwar cigaba da zaman Cancelo a Barcelona

Image
  Babu tabbas akan yiyuwar cigaba da zaman Cancelo a Barcelona. (Relevo) • Fagen Wasanni

Mulkin APC ya mayar da ma'aikatan Najeriya mabarata

Image
  ASALIN HOTON, PDp A Najeriya, babbar jam'iyyar hamayya ta kasar, wato PDP, ta yi kakkausar suka ga gwamnatin kasar ta jam'iyyar APC, game da karin albashin da gwamnatin ta yi, da cewa wani mataki ne na an yi ba a yi ba. Domin kuwa jam'iyyar PDPn na ganin an yi karin albashin ne yayin da jama'ar Najeriya ke ta fama da matukar tsadar man fetur da tsadar kayan abinci da dai sauran matsalolin da suka haifar da tsadar rayuwa. A ranar Talata, kwana ɗaya kafin ranar bikin ma'aikata ta duniya ne ofishin kula da albashin ma'aikata na Najeriya ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa an yi wa ma'aikatan gwamnatin tarayya ƙarin albashi da kashi 25 zuwa 35 cikin ɗari. Lamarin ya haifar da cece-ku-ce ganin cewa akwai wani kwamiti da gwamnatin ta kafa wanda aka ɗora wa alhakin samun matsaya kan albashi mafi ƙaranci a ƙasar.

Kun yarda Mata?

Image
 Kun yarda zaman da mata ke yi suna kula da ƴaƴa da iyali aiki ne da ya kamata a biya su albashi duk wata - Zuwairiyyah Adamu Girei

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta ki

Image
 Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta ki amincewa da karin albashin kashi 35%, da Gwamnatin tarayya tayiwa ma'aikatanta.

Gwamna Abba na Kano na Shirin Inganta noma da sana'o'i a tsarin zamani matakin duniya.

Image
  Gwamna Abba na Kano na Shirin Inganta noma da sana'o'i a tsarin zamani matakin duniya. A wani bangare na kudrin Neman Yakin Neman zabensa na inganta noma da kuma ciyar da jihar Kano gaba, Masana na cewa kara zuba jarin noma da Gwamna Abba K. Yusuf ya yi zai iya samar da gagarumin ci gaba. Waɗannan fa'idodin sun haɗa da haɓaka kudaden shiga na karkara, inganta wadatar abinci, samar da abinci mai araha da abinci mai gina jiki ga al'ummar Afirka da ke ci gaba da haɓakawa da inganta dorewar muhalli ta hanyar sabbin dabaru irin su noman zamani. Bugu da kari, gwamnatin Gwamna Yusuf ta ba da fifiko wajen karfafa gwiwar matasa ta hanyar farfado da cibiyoyin koyar da sana’o’i guda 26 a fadin jihar, ta yadda za a bunkasa sana’o’i. Daily hausa

Kwamitin da gwamnatin Kano

Image
  Kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa domin bincikar Ganduje ya fara zamansa a kotun  jihar kano  da ke sakatariyar Audu Bako Kanawapostnews

Yadda Aka kama ma'aikacin gidan gyaran hali Hamisu Mamuda

Image
Yayin da kokarin kaiwa fursunoni Tabar Wiwi a Kano. Kakakin Rundunar SP Abdullahi Haruna kiyawa ya ce sun tura wanda ake zargin mai kimanin shekara 52 zuwa sashin manyan bincike dake Bompai  

ƁAƘAR SAFIYA: Malama yau naga bakar safiya,

Image
   ba fada ba komai mijina bayan yayi sallar Asuba ya mikomin takardar saki, kuma Wallahi lafiya lau muke, jiya tare muka ci Abincin dare muna cu muna hira ina ta saka shi nishada da walwala, don kwanan nan sai Naga ya zauna shi kadai Yana tunani kamar Yana da damuwa in na tambaye shi sai yace ba komai. Da na karanta takardar na dago kai muka hada ido idanuwa na cike da kwalla nace masa wane mai nayi Maka ? Mai yayi zafi haka? Sai yace min zama ne ya kare kawai . Nayi hakuri. Da ya ga kukana ya tsanan ta sai yace wance kiyi hakuri ba son kine bana yiba, Amman Malamai na sun tabbatar min da cewa in har ina tare dake bazantaɓa yin arziki ba, sai dai na samu mai suna Safiyyya na aura shine burujin sunan mu zai haɗu. Malama Ya zanyi? Ni marainiyata ce , yarana uku,yanzu ma watana biyu da haihuwa ta ukun. Babata da babana duk sun rasu na rasa yadda zanyi.😭 Kanawapostnews

SHIN KANA BUSINESS ONLINE AMMA BAKASAN YANDA ZAKA SARRAFA SHI A ONLINE BA?!

Image
KANA KOYAN ABUBUWA A ONLINE AMMA BAKASAN YANDA ZAKA SAMU MUTANE KA KOYAR MUSU BA?! SHIN STUDENT NE KAI/KE KO MATAR AURE KO MATASHIYA/ MATASHI DAKE NEMAN ABUNYI DA WAYA A ONLINE?! TO KU KWANTAR DA HANKALINKU KOMAI YAZO KARSHE INSHA ALLAH!! KUYI JOINING GROUP INDA ZAKU KOYI WHATSAPP DIGITAL MARKETING DA YADDA ZAKU BUNKASA HARKOKIN KU TA ONLINE KUMA KU SAMU AKALLA 100K/ 200k DUK WATA DANNA LINK ƊIN DON SAMUN SHIGA✅ https://chat.whatsapp.com/ICZPG9TwKJt97w89evaMTw

Makarantar da ake zargin Yahaya Bello ya biya kuɗin karatun 'ya'yansa ta mayar wa EFCC kuɗin

Image
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ta ce makarantar 'American international school' da ke Abuja ta tura dala $760, 910.84 zuwa cikin asusun hukumar. Kuɗin wani ɓangare na dala 845,852 da ake zargin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya biya a makarantar don karatun 'ya'yansa biyar da za su yi a makarantar nan gaba. Mai magana da yawun hukumar, Wale Oyewale ya shaida wa BBC cewa tun da farko makarantar ta rubuta wa hukumar takardar cewa za ta mayar da kuɗin zuwa asusun gwamnati kasancewar hukuma na bincike a kan lamarin. Daga nan ne kuma EFCC ta aike wa makarantar asusun da ta sanya kudin a ciki, kamar yadda mista Oyewale ya bayyana . A ranar 18 ga watan Afrilu ne dai hukumar EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa-a-jallo, sakamakon zarginsa da ɓarnatar da kuɗaɗen gwamnatin jihar kogi a lokacin da yake jagorantar jihar. Bayan hakan ne kuma hukumar shige da fice ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa tana umartar jami'an hukumar da su kama shi a