Posts

Showing posts from March 2, 2024

Ƴanbindiga sun tayar da wasu garuruwan Katsina

Image
Ƴanbindiga masu satar mutane sun tilasta wa al'ummar wasu garuruwa a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya yin gudun hijira. Yanbindigar sun abka ne garin Wurma da ke ƙaramar hukumar Kurfi inda suka bude wuta, lamarin da ya tilasta wa mutanen yankin gudun hijira domin tsira da ransu zuwa makwabta. "Babu kowa a garin duka an fito," kamar yadda wani mazauni garin Wurma ya shaida wa BBC Gwamnatin jihar Katsina da ta tabbatar da al'amarin ta ce matsalar ta kuma shafi garuruwan Lambo da Guda da ke yankin na Kurfi. Kwamishinan tsaron jihar Katsina Dakta Nasir Baangida Ma'azu ya ce ƴanbindigar sun matsawa yankin. "Shiga ta farko sun bi gida-gida, shiga ta biyu kuma suka ƙone sansanin ƴansanda, dalilin da ya sa mutane suka gudo," a cewar Kwamishinan. A ranar Juma'a wasu al'ummar yankunann na karamar hukumar Kurfi sun gudanar da zanga-zanga kan kan ƙamarin matsalar tsaron da ke addabarsu. Sun ce an kashe mutane da sace d