Posts

Showing posts from May 11, 2024

DA DUMI-DUMI: EFCC ta dakatar da amfani da Dala, ta umurni Ofisoshin Jakadanci su koma ƙarbar Naira

Image
  DA DUMI-DUMI: EFCC ta dakatar da amfani da Dala, ta umurni Ofisoshin Jakadanci su koma ƙarbar Naira Hukumar EFCC ta umurci ma’aikatan kasashen waje da ke Najeriya da ofisoshin Jakadanci, su daina mu’amala da kudaden waje, su koma yin amfani da Naira wajen gudanar da harkokinsu na hada-hadar kudi,  A Yau ta ruwaito EFCC ta kuma umarci ma’aikatan Najeriya da ke kasashen waje da su karbi Naira a kasuwancinsu na kudi. Hukumar ta ce ta dauki matakin ne domin magance matsalar dala a tattalin arzikin Najeriya da kuma tabarbarewar darajar Naira. LIKE // SHARE & FOLLOW US >

Kamfanoni ne ya kamata su biya harajin tsaron intanet ba mutane ba

Image
  ASALIN HOTO Dama tun tuni akwai dokar tattara harajin tsaro ta intanet a Najeriya, yanzu ne kawai aka fara neman aiwatar da ita, wadannan sune kalaman masanin tattalin arziki Aliyu Da'u Aliyu. Ya bayyana hakan ne a cikin shirin Ra'ayi Riga na BBC Hausa da ake gabatarwa a kowacce Juma'ar ƙarshen mako. Shirin wanda ya samun bakuncin Sanata Shehu Umar Buba wanda ya gabatar da kudurin a gaban majalisar dattijan Najeriya da Honarabil Ali Madakin Gini dan Majalisar wakilan Najeriya da Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Consulting kuma masani kan harkokin tsaro da Malam Adam Hassan shugaban kungiyar 'yan tireda na arewacin Najeriya. Yayin tattaunawar da aka yi Aliyu Da'u Aliyu ya ce a mahangarsu ta tattalin arziki babu bukatar ƙara ƙaƙabawa dan Najeriya ƙarin haraji a yanzu, musamman idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a ƙasar. Shi kuwa Honarabil Ali Madakingini cewa ya yi, dokar ba ta shafi daidaikun mutane ba. "Ta taƙaita ne kan kamfanonin sadar...

Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Katsina

Image
 ‘Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Katsina Rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun yi nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Faskari da Malumfashi a jihar, a ranakun 8 da 9 ga watan Mayun 2024. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce ‘yan bindigar sun kai harin farko ne a ranar 8 ga watan Mayu, 2024, bayan sun tare hanyar Funtua zuwa Gusau, a kauyen Unguwar Boka, a karamar hukumar Faskari. A cewarsa, ‘yan ta’ad-dan sun far wa fasinjojin da ke tafiya a cikin wata kirar motar Golf III, inda suka ci da halbe-halbe. Sai dai Sadiq ya bayyana cewa shirin nasu ya ci tura sakamakon wani dauki da jami’an sintiri suka kai. Daily news hausa

WATA SABUWA: Tallafin man fetur da Tinubu ya dawo da shi zai kwashe kusan rabin kudin man fetur da Najeriya za ta sayar – inji IMF

Image
 WATA SABUWA: Tallafin man fetur da Tinubu ya dawo da shi zai kwashe kusan rabin kudin man fetur da Najeriya za ta sayar – inji IMF Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF ya yi gargaɗin cewa maido da tallafin man fetur da Najeriya ta yi zai laƙume kusan rabin kudaden shigarta na man fetur a bana, wanda hakan zai hana Gwamnati samun damar aiwatar da ayyukan da ta tsara za ta yi a bana, A cewar IMF tallafin zai janyo wa Najeriya hasarar kudin danyen mai na kusan fiye da dala tiriliyan 8.43 (dala biliyan 5.9) daga cikin kudin da ƙasar ta yi hasashen za ta samu na naira tiriliyan 17.7 na kudin man fetur, in ji IMF a wani rahoto da ta fitar... Daga shafin, A Yau