Posts

Showing posts from April 21, 2024

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Image
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai buɗe  taron yaƙi da ta'addanci na Afirka da za a gudanar a Abuja fadar gwamnatin ƙasar. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce taron - wanda Najeriya da haɗin gwiwar ofishin yaƙi da ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya suka shirya - za a fara shi ranar Litinin 22 ga watan Afrilu. Manufar taron ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa don yaƙi da ta'addanci a ƙasashen Afirka tare da sake fasalin yadda duniya ke kallon ta'addanci a Afirka, da kuma lalubo sabbin hanyoyin magance matsalar a faɗin nahiyar. Ana sa ran shugabannin gwamnatoci da manyan jami'an gwamnatocin ƙasashen Afirka, da wakilan ƙungiyoyin duniya da cibiyoyi, da jami'an diplomasiyya da ƙungiyoyin fararen hula za su halarci taron. Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed za ta halarci taron. ''Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malla