Posts

Showing posts from April, 2024

Gwamna Abba na Kano na Shirin Inganta noma da sana'o'i a tsarin zamani matakin duniya.

Image
  Gwamna Abba na Kano na Shirin Inganta noma da sana'o'i a tsarin zamani matakin duniya. A wani bangare na kudrin Neman Yakin Neman zabensa na inganta noma da kuma ciyar da jihar Kano gaba, Masana na cewa kara zuba jarin noma da Gwamna Abba K. Yusuf ya yi zai iya samar da gagarumin ci gaba. Waɗannan fa'idodin sun haɗa da haɓaka kudaden shiga na karkara, inganta wadatar abinci, samar da abinci mai araha da abinci mai gina jiki ga al'ummar Afirka da ke ci gaba da haɓakawa da inganta dorewar muhalli ta hanyar sabbin dabaru irin su noman zamani. Bugu da kari, gwamnatin Gwamna Yusuf ta ba da fifiko wajen karfafa gwiwar matasa ta hanyar farfado da cibiyoyin koyar da sana’o’i guda 26 a fadin jihar, ta yadda za a bunkasa sana’o’i. Daily hausa

Kwamitin da gwamnatin Kano

Image
  Kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa domin bincikar Ganduje ya fara zamansa a kotun  jihar kano  da ke sakatariyar Audu Bako Kanawapostnews

Yadda Aka kama ma'aikacin gidan gyaran hali Hamisu Mamuda

Image
Yayin da kokarin kaiwa fursunoni Tabar Wiwi a Kano. Kakakin Rundunar SP Abdullahi Haruna kiyawa ya ce sun tura wanda ake zargin mai kimanin shekara 52 zuwa sashin manyan bincike dake Bompai  

ƁAƘAR SAFIYA: Malama yau naga bakar safiya,

Image
   ba fada ba komai mijina bayan yayi sallar Asuba ya mikomin takardar saki, kuma Wallahi lafiya lau muke, jiya tare muka ci Abincin dare muna cu muna hira ina ta saka shi nishada da walwala, don kwanan nan sai Naga ya zauna shi kadai Yana tunani kamar Yana da damuwa in na tambaye shi sai yace ba komai. Da na karanta takardar na dago kai muka hada ido idanuwa na cike da kwalla nace masa wane mai nayi Maka ? Mai yayi zafi haka? Sai yace min zama ne ya kare kawai . Nayi hakuri. Da ya ga kukana ya tsanan ta sai yace wance kiyi hakuri ba son kine bana yiba, Amman Malamai na sun tabbatar min da cewa in har ina tare dake bazantaɓa yin arziki ba, sai dai na samu mai suna Safiyyya na aura shine burujin sunan mu zai haɗu. Malama Ya zanyi? Ni marainiyata ce , yarana uku,yanzu ma watana biyu da haihuwa ta ukun. Babata da babana duk sun rasu na rasa yadda zanyi.😭 Kanawapostnews

SHIN KANA BUSINESS ONLINE AMMA BAKASAN YANDA ZAKA SARRAFA SHI A ONLINE BA?!

Image
KANA KOYAN ABUBUWA A ONLINE AMMA BAKASAN YANDA ZAKA SAMU MUTANE KA KOYAR MUSU BA?! SHIN STUDENT NE KAI/KE KO MATAR AURE KO MATASHIYA/ MATASHI DAKE NEMAN ABUNYI DA WAYA A ONLINE?! TO KU KWANTAR DA HANKALINKU KOMAI YAZO KARSHE INSHA ALLAH!! KUYI JOINING GROUP INDA ZAKU KOYI WHATSAPP DIGITAL MARKETING DA YADDA ZAKU BUNKASA HARKOKIN KU TA ONLINE KUMA KU SAMU AKALLA 100K/ 200k DUK WATA DANNA LINK ƊIN DON SAMUN SHIGA✅ https://chat.whatsapp.com/ICZPG9TwKJt97w89evaMTw

Makarantar da ake zargin Yahaya Bello ya biya kuɗin karatun 'ya'yansa ta mayar wa EFCC kuɗin

Image
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ta ce makarantar 'American international school' da ke Abuja ta tura dala $760, 910.84 zuwa cikin asusun hukumar. Kuɗin wani ɓangare na dala 845,852 da ake zargin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya biya a makarantar don karatun 'ya'yansa biyar da za su yi a makarantar nan gaba. Mai magana da yawun hukumar, Wale Oyewale ya shaida wa BBC cewa tun da farko makarantar ta rubuta wa hukumar takardar cewa za ta mayar da kuɗin zuwa asusun gwamnati kasancewar hukuma na bincike a kan lamarin. Daga nan ne kuma EFCC ta aike wa makarantar asusun da ta sanya kudin a ciki, kamar yadda mista Oyewale ya bayyana . A ranar 18 ga watan Afrilu ne dai hukumar EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa-a-jallo, sakamakon zarginsa da ɓarnatar da kuɗaɗen gwamnatin jihar kogi a lokacin da yake jagorantar jihar. Bayan hakan ne kuma hukumar shige da fice ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa tana umartar jami'an hukumar da su kama shi a

Gini mai hawa biyu ya rufta kan magina fiye da 15 a Kano

Image
  Ana fargabar wani gini mai hawa biyu da ya ruguje ya faɗa kan wasu magina da ake aikin gini a yankin Kuntau da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano. Wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa ginin ya rufta kan magina fiye da 15. Tuni dai masu aikin ceto suka fara zaƙulo mutanen da suka maƙale a ginin. Zuwa lokacin da BBC ta yi magana da majiyarta, an zaƙulo mutum uku sai dai ɗaya a cikinsu ya mutu yayin da biyun ke cikin mawuyacin hali. Kawo yanzu dai ba a tantance adadin mutanen da ibtila'in ya rutsa da su ba. Article share tools View more share options Share this post Copy this link Karanta karin bayanai kan wannan mashigin

An janye ƴan sandan da ke samar da tsaro ga hukumar da Muhuyi ke jagora

Image
😳   O Copyright: FACEBOOK/MUHUYI MAGAJI RIMIN GADO Babban sufeton ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya janye ƴan sanda kimanin 40 da ke samar wa hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano tsaro. Matakin ya zo ne bayan binciken badaƙalar kuɗi da hukumar, ƙarƙashin jagorancin Muhuyi Magaji Rimin Gado take yi kan shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa babban sufeton ƴan sandan ya bayar da umarnin janye ƴan sandan ga kwamishinan yan sanda na jihar Kano, Usaini Gumel. Wata majiya da jaridar ta ruwaito ta ce wasu cikin ƴan sandan suna taimaka wa hukumar ta yaƙi da rashawa a Kano a binciken da take yi tare da samar da tsaro ga hedikwatar hukumar da sauran dukiyoyin da ake bincike a kansu. Article share tools View more share options Share this post Copy this link Karanta karin bayanai kan wannan mashigin

Sojin Najeriya sun kashe jagoran 'yan fashin daji a jihar Sokoto

Image
Copyright: Nigeria Army Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe wani jagoran 'yan fashin daji a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar. Wata sanarwa da ta fitar a shafukanta na intanet ta ce dakarun rundunar da aka tura don yaƙi da ta'addanci ne suka yi nasarar kashe jagoran, wanda ba ta bayyana sunansa ba, a ranar Laraba. "Bayan samun bayanan sirri, dakaru sun yi wa gungun 'yanta'addan kwanton-ɓauna a wata mashiga da ke ƙauyen Sarma a ƙaramar hukumar Tangaza, inda suka yi nasarar kashe jagoransu tare da ƙwato bindigar AK-47 da kuma babur," in ji sanarwar. A jihar Kaduna kuma, dakarun sojin sun yi nasarar katse hanzarin masu garkuwa da mutane a garin Kafanchan na ƙaramar hukumar Jema'a, sannan suka kama biyu daga cikinsu tare da ƙwato bindiga ɗaya, da harsasai, da kuma babur. Kazalika, wani ɗan fashi ya gamu da ajalinsa a wurin duba ababen hawa na Kaskara da ke ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato, lokacin da dakarun suka amsa kiran neman agaj

Zan yi murabus idan na gaza kai ƙarshen binciken Yahaya Bello – Shugaban EFCC

Image
  Zan yi murabus idan na gaza kai ƙarshen binciken Yahaya Bello – Shugaban EFCC Copyright: EFCC/X Shugaban hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa, Ola Olukoyede ya sha alwashin yin murabus idan na gaza gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello. A wani taron tattaunawa da zaɓaɓɓun editoci a hedikwatar hukumar da ke Abuja, babban birnin Najeriya, shugaban hukumar ya yi alƙawarin hukunta duk masu kawo kawo tarnaƙi ga kama tsohon gwamnan. A ranar 18 ga watan Afrilu, EFCC ta ayyana Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo saboda zarginsa da badaƙalar kuɗi ta naira miliyan 80. Yahaya Bello dai bai bayyana gaban kotu ba tun bayan ayyana ana nemansa ruwa a jallo. Shugaban EFCC ya ce da kansa ya kira Bello cikin mutunci inda ya nemi da ya bayyana gaban hukumar ya kuma yi bayani kan tuhume-tuhumen da ake masa. Shugaban EFCC ya ce duk da kiran wayar, tsohon gwamnan bai amsa gayyatar ba. Yahaya Bello dai ya musanta gayyatar da aka yi masa inda ya ƙalubala
Image
Copyright: Getty Images Kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki ya gayyaci ministan lantarki a Najeriya, Adebayo Adelabu da hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasar NERC da su bayyana gabansa a wani zaman bincike da za a yi game da ƙarin kuɗin lantarkin da aka yi a baya-bayan nan. Shugaban kwamitin majalisar, Sanata Enyinnaya Abaribe ne ya bayyana haka yayin gudanar da ayyukan kwamitin da kuma kai ziyara zuwa ma'aikatar lantarki da ke Abuja. Abaribe ya ce majalisar dattawa tuni ta amince a yi zaman ranar 29 ga watan Afrilu inda hukumomin gwamnati za su amsa tambayoyi. Ministan ya bayyana tarin matsalolin da suka addabi ɓangaren lantarki a Najeriya da suka haɗa da rashin isassun kuɗi da rashin iskar gas inda ya buƙaci kwamitin da ya tallafa wa ma'aikatar lantarki domin cimma ƙudurorinta. Kwamitin majalisar ya kuma duba wani aikin samar da wuta a harabar ma'aikatar. Sanata Abaribe ya kuma bayyana damuwa kan duk da maƙudan kuɗin da ake zubawa a ɓangaren lantarki, masu ruw

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Image
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai buɗe  taron yaƙi da ta'addanci na Afirka da za a gudanar a Abuja fadar gwamnatin ƙasar. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce taron - wanda Najeriya da haɗin gwiwar ofishin yaƙi da ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya suka shirya - za a fara shi ranar Litinin 22 ga watan Afrilu. Manufar taron ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa don yaƙi da ta'addanci a ƙasashen Afirka tare da sake fasalin yadda duniya ke kallon ta'addanci a Afirka, da kuma lalubo sabbin hanyoyin magance matsalar a faɗin nahiyar. Ana sa ran shugabannin gwamnatoci da manyan jami'an gwamnatocin ƙasashen Afirka, da wakilan ƙungiyoyin duniya da cibiyoyi, da jami'an diplomasiyya da ƙungiyoyin fararen hula za su halarci taron. Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed za ta halarci taron. ''Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malla