Posts

Showing posts from February 11, 2024

Tinubu ya ƙaddamar da sabbin jiregen yaƙi don magance matsalar tsaro

Image
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyarsa ta kawo ƙarshen mastalar tsaro a ƙasar ta hanyar ƙaddamar da wasu sabbin jirage masu saukar ungulu kirar T-129 ATAK guda biyu da kirar King Air 360ER Beechcraft a barikin sojin saman Najeriya da ke birnin Makurdi a jihar Benue.. Da yake magana ta bakin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima, shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar sayen waɗannan sabbin jiragen masu saukar ungulu domin inganta yaƙin da rundunar sojojin saman Najeriya ke yi a ƙasar da yankin yammacin Afirka. Badaru Abubakar, ministan tsaro ya yaba wa ƙoƙarin shugaba Tinubu na mayar da zaman lafiya a fadin ƙasar, ya kuma gode masa bisa jajircewarsa da goyon bayan da yake bai wa rundunar sojin ƙasar duk da kalubalen da take fuskanta.

Mun yi maganin masu bai wa ƴan bindiga bayanai-Gwamna Dikko Radda

Image
ASALIN HOTON, DIKKO RADDA/FACEBOOK Sa'o'i 5 da suka wuce Gwamnan jihar Katsina ya yi kira ga jama’ar jihar su tallafawa jami’an tsaro wajen yaƙi da ƴan bindiga da suka addabi sassan jihar. Gwamnan Umaru Dikko Radda ya ce akwai buƙatar mutane, musamman matasa su haɗa kansu domin tallafawa jami’an tsaro wajen aikin kawar da matsalar tsaron. A hirar sa da BBC, gwamnan ya kuma musanta rahotannin da ke cewa gwamnatinsa ta gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma yayin da ƴan bindiga ke cigaba da kai hare hare a wasu yankunan jihar. Gwamnan ya ce tun bayan da ya karɓi mulki, gwamnatinsa ta samu nasara sosai a yakin da take yi da ƴan bindiga, ciki har da kafuwar rundunar tsaro ta musaman wadda a cewarsa ta taimaka wajan dakile hare haren yan bindigar. Ya ce: "Mutumin Jibia da mutumin Batsari da na Kankara da na Danmusa da na Sabuwa da na Faskari da na Dandume sun san cewa an samu sauƙi a matsalar tsaron da muke fuskanta a jihar Katsina’’ Ya yi bayanin cewa sabbin dabarun...