Posts

Showing posts from February 25, 2024

Hatsaniya ta ɓarke tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda a Isra'ila

Image
Getty Images Copyright: Getty Images An samu hatsaniya a birnin Tel aviv na Isra'ila ya yin da ƴan sanda suka yi ƙoƙarin tarwatsa masu zanga-zangar neman a sako wadanda Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza. Ƴansandan sun riƙa tura masu zanga-zangar baya ta hanyar amfani da ruwan zafi tare da tare hanyar da za su bi. Hukumomi sun kama masu zanga-zangar 21. Masu Zanga-zangar kenan suke kira ga firai ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da ya sauka daga muƙaminsa tare da neman a gaggauta yin zaɓe.