Mahaifiyata abar alfarina
"Ana cewa kafin ka auri mace ka dubi wace ce mahaifiyarta, don akwai tsammani nason ɗabi'a, shawara ce mai kyau. Idan tana zaune da kishiya, ya mu'amalarsu take? Wacce irin kuɗuba take yi wa 'ya'yanta? Idan akwai yayar yarinya da ta yi aure, ya 'interferance' na mahaifiyyar yake a gidan auren 'ya'yanta... ka duba wannan, ba iya soyayya ba. Ita ma mace! Yana da kyau ke ma ki duba alaƙar namiji da 'yan mahaifiyyarsa da 'yan uwansa mata. A zahiri a aikace, me ya ɗauki mace? 'Yar tsana (toy) ko mutum? Yana tausayinsu? Yana taimaka musu? Wannan ɗabi'a zai Ku rabu da gigi da giyar soyayyar mai bugarwa, a marhalar soyayya kowa 'perfection' nasa yake ƙoƙarin nunawa don ya samu karɓuwa, tare da ƙoƙarin lulluɓe naƙasunsa a halayya da ɗabi'a, saboda a marhalar nema ana tsayuwa ne na ɗan lokaci. Halayya kuma ba ta ɓoyewa, saboda ita ce ke sarrafa gaɓɓan jikinmu sai hali ya bayyana komai tsawon lokacin zama na dindindin. Da yake Ub...