Majalisar wakilan Najeriya za ta ƙarfafa dokar ɓata-sunaKakakin majalisar wakilan Najeriya,
Tajudeen Abbas ya ce majalisar za ta ƙarfafa dokar ɓata-suna da cin cin mutuncin mutane da kuma cin zarafin mutane ta intanet. Honarabul Tajedeen ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai kan abubuwan da ke damun ƙasar da aka gudanar a wani ɗakin taro a harabar majalisar. Kakakin majalisar ya ce manufar dokar ba zai ci karo da 'yancin faɗar albarkacin baki, amma za ta kare mutane da hukumomi daga cin zarafinsu a intanet. Ya ƙara da cewa dole ne 'yan Najeriya su damu bisa yadda ake yawan cin zarafin jami'an gwamnati a shafukan intanet. Honarabul Abbas ya bayyana yadda kakakin majalisar da ya gabace shi, Femi Gbajabiamila, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fuskanci cin zarafi da intanet, da ɓata suna