Posts

Showing posts from April 10, 2024

Yau take sallah barka da sallah

Image
Ya ce ƙwarewarsu da rashin bai wa abokan kulɗa kunya wajen shirya abincin fita-kunya kamar tuwon sallah cikin gwaninta sun sa mutane na ƙara neman ƙwararrun masu dafa abinci. Ko ba komai, in ji shi, ba a ko'ina ake samun ɗanɗano da daɗi da iya tsara dafaffen abinci mai rai da lafiya a kwano, da ƙamshin burgewa ba. "A kawo muku har gida, ba tare da kun san wata wahalar da aka yi ba, kawai ci kuka sani" in ji mai gidan abincin. "Sai dai ku ci, ku ji daɗi, shi ma wanda aka ba, ya ci ya ji daɗi. Sai a yi ta tunanin ta yaya aka yi haka?" Mata da yawa kamar Ni'ima Ibrahim, ba lallai su yarda da wannan ra'ayi ba. Suna ganin duk da zamani, amma girki ya fi yarda da hannun mata. Hatta naƙaltar yadda ake shirya tuwon sallah, ba abu ne da ke buƙatar wuta-wuta da riƙon maza ba. Gwanintar mata ta fi tashi a girkin tuwon sallah Mata suna bai wa girkin tuwon sallah wata kulawa ta musamman, cewar Dr Hadiza Koko. "Mace du wadda take, in aka ce tuwon sallah za ta yi.