Yadda cire tallafin lantarki a Najeriya zai shafe ku idan farashin ya ninka uku
Hukumomi a Najeriya na shirin cire kashi 15% na tallafin da suke biya wajen samar da lantarki, a wani ɓangare na jerin sauye-sauye don rage kashe kuɗaɗen gwamnati. Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya ambato mai magana da yawun shugaban ƙasa, Mista Bayo Onanuga na cewa matakin zai kai ga rage kuɗi sama da naira tirliyan uku da gwamnati take kashewa. Ya ce gwamnati na fuskantar matsin lamba don ta bari a ƙara farashin lantarki, saboda ita kawai ta ware naira biliyan 450 a matsayin tallafi ne a bana. Sai dai ya ce ba kowa da kowa cire tallafin zai shafa ba, masu amfani da wutar lantarki kashi 15 ne kawai, amma kuma su ne ke shan kashi 40% na wutar lantarki a Najeriya matakin zai shafa. Ko da yake bai ce ga ranar da sabon ƙarin kuɗin lantarkin zai fara aiki ba, amma ya ce da zarar hakan ta kasance gwamnati na sa ran tattalin kuɗi kusan naira tirliyan 1.1 duk shekara. Sai dai kafar yaɗa labarai ta Bloomberg ta ruwaito wata majiya da ke cewa ƙarin zai fara aiki ne a cikin wannan wata na ...