Yadda cire tallafin lantarki a Najeriya zai shafe ku idan farashin ya ninka uku
Hukumomi a Najeriya na shirin cire kashi 15% na tallafin da suke biya wajen samar da lantarki, a wani ɓangare na jerin sauye-sauye don rage kashe kuɗaɗen gwamnati.
Kamfanin dillanci labarai na Reuters ya ambato mai magana da yawun shugaban ƙasa, Mista Bayo Onanuga na cewa matakin zai kai ga rage kuɗi sama da naira tirliyan uku da gwamnati take kashewa.
Ya ce gwamnati na fuskantar matsin lamba don ta bari a ƙara farashin lantarki, saboda ita kawai ta ware naira biliyan 450 a matsayin tallafi ne a bana. Sai dai ya ce ba kowa da kowa cire tallafin zai shafa ba, masu amfani da wutar lantarki kashi 15 ne kawai, amma kuma su ne ke shan kashi 40% na wutar lantarki a Najeriya matakin zai shafa.
Ko da yake bai ce ga ranar da sabon ƙarin kuɗin lantarkin zai fara aiki ba, amma ya ce da zarar hakan ta kasance gwamnati na sa ran tattalin kuɗi kusan naira tirliyan 1.1 duk shekara.
Sai dai kafar yaɗa labarai ta Bloomberg ta ruwaito wata majiya da ke cewa ƙarin zai fara aiki ne a cikin wannan wata na Afrilu.
Kuma matakin zai bai wa kamfanonin samar da lantarki damar ƙara farashin lantarki zuwa naira 200 daga naira 68 a kan duk kilowat ga masu amfani da wutar lantarki a yankunan birane.
Bashi ya yi wa gwamnati yawa
Tun a tsakiyar watan Fabrairu ne, ministan lantarki na Najeria, Adebayo Adelabu ya sanar da cewa ƙasar ba za ta iya ci gaba da biyan tallafi a kan wutar lantarki ba saboda tarin basukan da kamfanonin samar da lantarki ke bin gwamnati.
Ya ce basukan da kamfanonin wuta da masu samar da iskar gas ke bin gwamnati sun zarce naira tiriliyan uku.
A cewarsa, ɗaukan matakin ya zama dole domin gwamnati ta samu damar magance basukan da ke kanta waɗanda ke ƙaruwa.
Sanarwar ta Adelabu ta janyo ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta kasancewar har yanzu ƴan Najeriya na fuskantar tarin ƙalubale tun bayan da gwamnatin Bola Tinubu ta janye tallafin man fetur - lamarin da ya jefa ƴan Najeriya cikin ƙangin rayuwa da hauhawar farashi.
Bari mu duba abin da matakin ke nufi da makomar lantarki idan aka cire tallafin da kuma irin tasirin da zai yi ga ƴan Najeriya.
Comments