Posts

Showing posts from March 22, 2024

Al'umma na gudun hijira a Zamfara Ƴan gudun hijira A

Image
Najeriya, 'yan bindiga na kara matsa kaimi a har-haren da suke kai wa wasu garuruwan Jangebe da Magazu na jihar Zamfara, inda suke sace mutane don neman kudin fansa, bayan sun aikata kisan gilla da barnata dukiyoyin jama'a. Matsalar hare-haren 'yan bindiga da ta addabi al'ummar garin Jangebe da wasu kauyukansa akalla biyar, a yankin karamar hukumar Talatar Mafara ta jihar Zamfara, ta kara kwabewa. A cewar wani mutumin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun daga ranar talata har zuwa laraba, kauyukan Jangebe biyar zuwa shida suna cikin iftila’in kashe-kashe. Mazaunin na Jangebe ya shaida wa BBC cewa a baya an samu saukin lamarin, sai dai kwanan nan abin ya dawo sabo a yankin Talatar Mafara ta Kudu, kuma yawacin mutanen kauyukan yankin, “Muna rokon gwamnatin tarayya da ta jiha su kawo mana dauki.” A garin Magazu na yankin karamar hukumar Tsafe ma, hare-haren 'yan bindigan suna kara munana, kamar yadda wani mutumin garin da ba ya so a fadi sunansa ya bayyana wa