Abinci bakwai da ƴan Najeriya suka sauya saboda tsadar rayuwa
Sa'o'i 3 da suka wuce Sakamakon tashin gwauron zabbin kayan masarufi da 'yan Najeriya ke fama da shi wanda matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta ya haifar, yanzu haka mutane da dama ba sa iya samun abinci sau uku a kullum. Bayanai sun nuna cewa su kansu wadanda suke samun ukun a kowace rana, sun sauya daga abin da suka saba ci a baya zuwa mai sauki wanda za a saya da kudi kadan sannan kuma zai cika ciki. Daga bayanai da kuma binciken da BBC ta yi a kasuwanni, ga wasu jerin abinci ko kuma kayan hadin abinci guda bakwai da yanzu jama'a suka sauya domin samun sa'ida: Shinkafa: Yanzu haka magidanta da dama sun koma amfani da wata nau'in shinkafa da ake wa lakabi da "A Fafata". Ita wannan shinkafar dai ta yi kama da wadda a zamanin baya lokacin wadata ake kira "dameji" wato wadda kamfani ya fitar saboda ta lalace. Bayanai sun nuna ana sayar da kwanon irin wannan shinkafa ta "A fafata" naira dubu biyu da dari biyar. ASALIN HOTON, ...