Posts

Showing posts from March 8, 2024

Kano Za Ta Haɗa Gwiwa Da Afrinvest Don Haɓɓaka Kasuwanci Da Ci Gaban Jihar

Image
  Kanawapostnews Gwamnatin jihar Kano ta bayyana aniyarta na hadin gwiwa da kamfanin Afrinvest (West Africa) Limited domin inganta harkokin kasuwanci da ci gaban jihar. Gwamna Abba Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a bikin bude ofishin Afrinvest na Kano a ranar Alhamis. Gwamnan wanda ya samu wakilcin Babban Sakatare a Ma’aikatar Kudi, Kabiru Sa’id Magami, ya bayyana cewa, babu wani lokaci da ya fi dacewa da Afrinvest ta kafa ofishi a jihar fiye da yanzu. Gwamnan ya taya kungiyar Afrinvest murna kan nasarorin da ta samu a cikin shekaru 30 da suka gabata da kuma zaben Kano a matsayin daya daga cikin wuraren da ta kafa zango. Gwamna Yusuf ya kuma yi alkawarin cewa, gwamnatin jihar za ta baiwa kamfanin duk wani tallafi da ya dace.