Makarantar da ake zargin Yahaya Bello ya biya kuɗin karatun 'ya'yansa ta mayar wa EFCC kuɗin
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ta ce makarantar 'American international school' da ke Abuja ta tura dala $760, 910.84 zuwa cikin asusun hukumar. Kuɗin wani ɓangare na dala 845,852 da ake zargin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya biya a makarantar don karatun 'ya'yansa biyar da za su yi a makarantar nan gaba. Mai magana da yawun hukumar, Wale Oyewale ya shaida wa BBC cewa tun da farko makarantar ta rubuta wa hukumar takardar cewa za ta mayar da kuɗin zuwa asusun gwamnati kasancewar hukuma na bincike a kan lamarin. Daga nan ne kuma EFCC ta aike wa makarantar asusun da ta sanya kudin a ciki, kamar yadda mista Oyewale ya bayyana . A ranar 18 ga watan Afrilu ne dai hukumar EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa-a-jallo, sakamakon zarginsa da ɓarnatar da kuɗaɗen gwamnatin jihar kogi a lokacin da yake jagorantar jihar. Bayan hakan ne kuma hukumar shige da fice ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa tana umartar jami'an hukumar da su kama shi a...