Posts

Showing posts from February 3, 2024

INEC ta dakatar da zaɓen cike giɓi a wasu rumfunan Kano da Enugu da Akwa Ibom

Image
Kanawa post news  Hukumar zaɓen Najeriya ta sanar da dakatar da zaɓukan cike giɓi da ake gudanarwar a jihohin Kano da Enugu da Akwa Ibom. Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon matsalolin da aka samu na satar da kayan zaɓe da yin garkuwa da wasu jami'an zaɓe a jihohin. Sanarwar ta ce wuraren da lamarin ya shafa sun haɗar da rumfuna biyu a mazaɓar tarayya ta Ikono/Ini a jihar Akwa Ibom, inda INEC din ta ce aka samu wasu ɓata-gari suka lalata kayan zaɓen. A jihar Enugu kuwa da ke kudu maso gabashin ƙasar, hukumar zaɓen ta ce an fitar da takardun sakamako tun kafin fara zaɓe a rumfuna takwas. A ƙananan hukumomin Kunchi da Tsanyawa kuma, INEc din ta ce an samu hatsaniya a rumfunan zaɓe 10, inda 'yan daba suka lalata kayan zaɓe tare da hana gudanar da zaɓen. Hukumar zaɓen ta ce ta yi aiki da sashen dokar zaɓen na 24 wajen dakatar da zaɓen. Hukumar ta kuma yi kira ga jami'an tsaro da su gudanar da bincike kan lamurran, inda hukumar ta ce tana

Syria ta zargi Amurka da iza wutar rikici a Gabas ta Tsakiya

Image
a Kanawa post news  Ma'aikatar Harkokin Wajen Syria ta yi Allah-wadai da harin da Amurka ta kai da daren jiya a Iraƙi da Syria. Cikin wata sanarwa da aka wallafa a kamfanin dillancin labarai na ƙasar SANA, ta ce harin da Amurka ta kai ya sake tabbatar da abin da ake zargi na cewa, dakarunta na barazana ga zaman lafiyar duniya, kuma ita take iza wutar rikicin da yake faruwa a yakin Gabas ta Tsakiya." Gwamnatin Syria dai na adawa da kasancewar Amurka a cikinta kuma tana ɗaukar hakan a matsayin mamaya. A bara ne Syria ta koma cikin ƙungiyar ƙasahen Larabawa, bayan sama da shekara 10 da aka koreta daga ƙungiyar saboda muguntar da ta nuna kan masu rajin dimokraɗiyya lokacin da suke zanga-zanga, wani abu da ya tayar da rikicin basasa. Amurka da Burtaniya da wasu sauran ƙasashen yamma sun soki komawar Syria cikin ƙungiyar, kuma a bayan nan sun jaddada cewa ba za su dawo hulɗar diflomasiyya ba da shugaban Syrian Shugaba Bashar al-Assad. Article share tools