INEC ta dakatar da zaɓen cike giɓi a wasu rumfunan Kano da Enugu da Akwa Ibom



Kanawa post news 

Hukumar zaɓen Najeriya ta sanar da dakatar da zaɓukan cike giɓi da ake gudanarwar a jihohin Kano da Enugu da Akwa Ibom.


Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon matsalolin da aka samu na satar da kayan zaɓe da yin garkuwa da wasu jami'an zaɓe a jihohin.


Sanarwar ta ce wuraren da lamarin ya shafa sun haɗar da rumfuna biyu a mazaɓar tarayya ta Ikono/Ini a jihar Akwa Ibom, inda INEC din ta ce aka samu wasu ɓata-gari suka lalata kayan zaɓen.


A jihar Enugu kuwa da ke kudu maso gabashin ƙasar, hukumar zaɓen ta ce an fitar da takardun sakamako tun kafin fara zaɓe a rumfuna takwas.


A ƙananan hukumomin Kunchi da Tsanyawa kuma, INEc din ta ce an samu hatsaniya a rumfunan zaɓe 10, inda 'yan daba suka lalata kayan zaɓe tare da hana gudanar da zaɓen.


Hukumar zaɓen ta ce ta yi aiki da sashen dokar zaɓen na 24 wajen dakatar da zaɓen.


Hukumar ta kuma yi kira ga jami'an tsaro da su gudanar da bincike kan lamurran, inda hukumar ta ce tana gudanar da cikakken bincike daga nata ɓangare, don gano ko jami'anta sun saɓa doka a ayyukansu.


INEC ta gargaɗi masu sa ido kan zaɓen Najeriya


Zaɓen cike giɓi: Ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a a Kaduna

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano