Posts

Recent post

Halin da makarantar firamare ta garin Bargi ke ciki a karamar hukumar Kiru.

Image
Halin da makarantar firamare ta garin Bargi ke ciki a karamar hukumar Kiru. Shekaru biyu bayan rahoton Premier Radio kan mummunan halin da makaranta ke ciki har yanzu ba abinda ya sauya.  

DA DUMI-DUMI: EFCC ta dakatar da amfani da Dala, ta umurni Ofisoshin Jakadanci su koma ƙarbar Naira

Image
  DA DUMI-DUMI: EFCC ta dakatar da amfani da Dala, ta umurni Ofisoshin Jakadanci su koma Æ™arbar Naira Hukumar EFCC ta umurci ma’aikatan kasashen waje da ke Najeriya da ofisoshin Jakadanci, su daina mu’amala da kudaden waje, su koma yin amfani da Naira wajen gudanar da harkokinsu na hada-hadar kudi,  A Yau ta ruwaito EFCC ta kuma umarci ma’aikatan Najeriya da ke kasashen waje da su karbi Naira a kasuwancinsu na kudi. Hukumar ta ce ta dauki matakin ne domin magance matsalar dala a tattalin arzikin Najeriya da kuma tabarbarewar darajar Naira. LIKE // SHARE & FOLLOW US >

Kamfanoni ne ya kamata su biya harajin tsaron intanet ba mutane ba

Image
  ASALIN HOTO Dama tun tuni akwai dokar tattara harajin tsaro ta intanet a Najeriya, yanzu ne kawai aka fara neman aiwatar da ita, wadannan sune kalaman masanin tattalin arziki Aliyu Da'u Aliyu. Ya bayyana hakan ne a cikin shirin Ra'ayi Riga na BBC Hausa da ake gabatarwa a kowacce Juma'ar Æ™arshen mako. Shirin wanda ya samun bakuncin Sanata Shehu Umar Buba wanda ya gabatar da kudurin a gaban majalisar dattijan Najeriya da Honarabil Ali Madakin Gini dan Majalisar wakilan Najeriya da Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Consulting kuma masani kan harkokin tsaro da Malam Adam Hassan shugaban kungiyar 'yan tireda na arewacin Najeriya. Yayin tattaunawar da aka yi Aliyu Da'u Aliyu ya ce a mahangarsu ta tattalin arziki babu bukatar Æ™ara Æ™aÆ™abawa dan Najeriya Æ™arin haraji a yanzu, musamman idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a Æ™asar. Shi kuwa Honarabil Ali Madakingini cewa ya yi, dokar ba ta shafi daidaikun mutane ba. "Ta taÆ™aita ne kan kamfanonin sadar

Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Katsina

Image
 ‘Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Katsina Rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun yi nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Faskari da Malumfashi a jihar, a ranakun 8 da 9 ga watan Mayun 2024. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce ‘yan bindigar sun kai harin farko ne a ranar 8 ga watan Mayu, 2024, bayan sun tare hanyar Funtua zuwa Gusau, a kauyen Unguwar Boka, a karamar hukumar Faskari. A cewarsa, ‘yan ta’ad-dan sun far wa fasinjojin da ke tafiya a cikin wata kirar motar Golf III, inda suka ci da halbe-halbe. Sai dai Sadiq ya bayyana cewa shirin nasu ya ci tura sakamakon wani dauki da jami’an sintiri suka kai. Daily news hausa

WATA SABUWA: Tallafin man fetur da Tinubu ya dawo da shi zai kwashe kusan rabin kudin man fetur da Najeriya za ta sayar – inji IMF

Image
 WATA SABUWA: Tallafin man fetur da Tinubu ya dawo da shi zai kwashe kusan rabin kudin man fetur da Najeriya za ta sayar – inji IMF Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF ya yi gargaÉ—in cewa maido da tallafin man fetur da Najeriya ta yi zai laÆ™ume kusan rabin kudaden shigarta na man fetur a bana, wanda hakan zai hana Gwamnati samun damar aiwatar da ayyukan da ta tsara za ta yi a bana, A cewar IMF tallafin zai janyo wa Najeriya hasarar kudin danyen mai na kusan fiye da dala tiriliyan 8.43 (dala biliyan 5.9) daga cikin kudin da Æ™asar ta yi hasashen za ta samu na naira tiriliyan 17.7 na kudin man fetur, in ji IMF a wani rahoto da ta fitar... Daga shafin, A Yau

Chelsea za ta yi nazari,kan makomar Pochettino, Flick zai koma Bayern Munich

Image
  GETTY IMAGES Bayanan hoto, Mauricio Pochettino Chelsea  za ta yi nazarin karshen kakar wasa ta bana bayan wasan karshe na gasar Premier da za ta yi da  Bournemouth , inda za ta yanke shawara kan makomar kocinta Mauricio Pochettino.  (Telegraph) Arsenal  na zawarcin tsohon mai tsaron ragar kungiyar da Poland Wojciech Szczesny, mai shekara 34, da golan Brighton Jason Steele dan Birtaniya da kuma na Ajax Diant Ramaj dan kasar Jamus yayin da su ke neman wanda zai maye gurbin Aaron Ramsdale, mai shekara 25 wanda zai bar Gunners.  (Standard) Har illa yau  Arsenal  na kuma duba yiwuwar daukar golan  Everton  da Ingila Jordan Pickford, mai shekara 30 a wannan bazara.  (Teamtalk) Gunners  na kuma neman dan wasan baya da tsakiya da kuma mai kai hari a kokarin da suke yi domin fadada 'yan wasan kungiyar karkashin jagorancin Mikel Arteta.  (Standard) Graham Potter ya ki amincewa da damar da aka bashi na zama kociyan Ajax, bayan da ya kasance wanda ke kan gaba a matsayin jagoran kungiyar ta N

#innalillahi... Abun yanamin ciwo araina inajin ba dadi. Idan na kalli rayuwata

Image
 #innalillahi... Abun yanamin ciwo araina inajin ba dadi. Idan na kalli rayuwata  Duniya tayi zafi rayuwa Tana neman yin juyin juya Hali..  Ilimi yazama tarihi a unguwanin mu..  Shin menene matsalar NE  A iya fahimtata masu kudin mu Da shuwagabanin mu sune basa kaunar ganiin muncigaba a Harkar ilimi  Sceince sunyi gsky dasuke cewa marabar Dan adam Da dabba shine tunani,hankali, dakuma kwakwalwa Da aikinta..  Ayau anwayi gari ana amfanin Da jahilicin mu wajen maidamu dabbobin kwantarwa ayanka  Ina ganin hakkin mutunne matukar yanada dabba yaciyar Da ita halak Mufa mutanene babu Wanda zai ciyar damu sai Allah.. Toh meyasa Ta karfi dayaji saikun maidamu dabbobi ta hanyar nesantamu Da ilimi   Rayuwar karatun talaka Da dayanxu  Before jamb 2500 but yanzu 5k  Before neco 25k yanzu Kuma 35k Before WA. Ec 30k yanxu 40k  Ana siyasantar mana Da ilimi haba  Yabaxamu jii ba dadiba  Wlh karkuyi tunanin muka Bari suka rabamu Da ilimi toh wann abubuwan su zasu karu  Yunwa zata yawaita  Tsanani zai ts

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya biya wa daukacin maniyyata aikin bana daga jihar kudin hadaya.

Image
 Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya biya wa daukacin maniyyata aikin bana daga jihar kudin hadaya. Kudin hadayar kowane Alhaji dai sun kama Riyale 720 kwatankwacin Naira 280,000

Sabon filin jirgin saman Dubai da za a kashe Dala bilyan 35 wajen gina shi

Image
  Sabon filin jirgin saman Dubai da za a kashe Dala bilyan 35 wajen gina shi, da za a kammala aikin rukunin farko a shekaru 10. DW Hausa