Kamfanoni ne ya kamata su biya harajin tsaron intanet ba mutane ba
Dama tun tuni akwai dokar tattara harajin tsaro ta intanet a Najeriya, yanzu ne kawai aka fara neman aiwatar da ita, wadannan sune kalaman masanin tattalin arziki Aliyu Da'u Aliyu.
Ya bayyana hakan ne a cikin shirin Ra'ayi Riga na BBC Hausa da ake gabatarwa a kowacce Juma'ar ƙarshen mako.
Shirin wanda ya samun bakuncin Sanata Shehu Umar Buba wanda ya gabatar da kudurin a gaban majalisar dattijan Najeriya da Honarabil Ali Madakin Gini dan Majalisar wakilan Najeriya da Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Consulting kuma masani kan harkokin tsaro da Malam Adam Hassan shugaban kungiyar 'yan tireda na arewacin Najeriya.
Yayin tattaunawar da aka yi Aliyu Da'u Aliyu ya ce a mahangarsu ta tattalin arziki babu bukatar ƙara ƙaƙabawa dan Najeriya ƙarin haraji a yanzu, musamman idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a ƙasar.
Shi kuwa Honarabil Ali Madakingini cewa ya yi, dokar ba ta shafi daidaikun mutane ba. "Ta taƙaita ne kan kamfanonin sadarwa na ƙasar".
Ya kuma ce wannan dalili ne ya sanya suka nemi majalisa ta dakatar da wannan shiri da CBN ya bullo da shi da aka bayar da wa'adin kwanaki biyu a fara aiwatar da shi.
"Matukar muna nan, za mu ga an aiwatar da dokar yadda ya kamata, ba za mu bar ko dan Najeriya daya ba ya biya kudin tsaron intanet," in ji Madakin Gini.
Shi kuwa Malam Adam Hassan cewa ya yi komai a ka kirkiro sai ya rika karewa kan 'yan kasuwa "a yanzu haka wata harkar idan ka yi ba za ka ci rabin kaso dayan da aka ce a rika cirewa ba a matsayin harajin tsaron zambar intanet,".
Masanan dai sun bayar da shawarwari masu yawa na yadda gwamnati za ta aiwatar da wannan tsare tsare ba tare da an muzgunawa talaka ba.
Da yake nasa bayanin Malam Kabiru Adamu masanin harkokin tsaro cewa ya yi babu shakka Najeriya na fuskantar barazanar tsaron intanet, lokaci zuwa lokaci kuma akan yi wa lamuran kasar kutse
Comments