ASALIN HOTON, PDp A Najeriya, babbar jam'iyyar hamayya ta kasar, wato PDP, ta yi kakkausar suka ga gwamnatin kasar ta jam'iyyar APC, game da karin albashin da gwamnatin ta yi, da cewa wani mataki ne na an yi ba a yi ba. Domin kuwa jam'iyyar PDPn na ganin an yi karin albashin ne yayin da jama'ar Najeriya ke ta fama da matukar tsadar man fetur da tsadar kayan abinci da dai sauran matsalolin da suka haifar da tsadar rayuwa. A ranar Talata, kwana ɗaya kafin ranar bikin ma'aikata ta duniya ne ofishin kula da albashin ma'aikata na Najeriya ya fitar da wata sanarwa inda ya bayyana cewa an yi wa ma'aikatan gwamnatin tarayya ƙarin albashi da kashi 25 zuwa 35 cikin ɗari. Lamarin ya haifar da cece-ku-ce ganin cewa akwai wani kwamiti da gwamnatin ta kafa wanda aka ɗora wa alhakin samun matsaya kan albashi mafi ƙaranci a ƙasar.