Posts

Showing posts from February 29, 2024

Muna tsare da shugabannin Binance a Najeriya'

Image
ASALIN HOTON, ALAMY 29 Fabrairu 2024, 07:36 GMT Wanda aka sabunta Sa'o'i 3 da suka wuce Gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa BBC cewar tana tsare da wasu manyan jami'an shafin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance a birnin Abuja. Hakan na zuwa ne bayan wasu rahotanni da suka ɓulla a daren ranar Laraba da ke nuna cewa hukumomi na tsare da jami'an. A wata tattaunawa da BBC, Zakari Mijinyawa, wanda shi ne shugaban sashen yaɗa labaru na ofishin mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, ya ce "ana yi wa jami'an tamnayoyi ne ƙarƙashin binciken da hukumomin tsaro ke yi kan daidata kasuwar musayar kuɗi, wanda ofishin na mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro ke jagoranta". Hukumomi na zargin shafin na Binance ne da laifin "ƙayyade farashin kuɗin ƙasashen waje a ƙasar". Darajar takardar kuɗin Najeriya dai ta yi faduwar da ba a taɓa gani ba a tarihi tun bayan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ƙyale kasuwa ta tantance darajarta. Lamarin ya ƙara jefa ta