Posts

Showing posts from March 7, 2024

An sace ɗalibai kusan '200' a ƙauyen Kuriga na jihar Kaduna

Image
An sace ɗaliban firamare da na sakandare kusan su 200 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya. Lamarin ya faru ne da safiyar yau (Alhamis) lokacin da ɗaliban ke taro (assembly) da misalin karfe takwas da rabi. Wani babban jami'in gwamnatin jihar Kaduna ya tabbatar wa BBC afkuwar lamarin amma ya ce ya zuwa yanzu babu cikakken bayani kan lamarin. Wani da ya shaida faruwar lamarin ya ce "yau da misalain ƙarfe 8:30 an gama asambili ke nan sai ga shigowar waɗannan mutane (ƴan fashi) daga kowane ɓangare, suka zo suka yi wa makarantar ƙawanya suka kwashi ɗalibai na firamare da sakandare kusan 200 suka wuce da su, har da malami ɗaya na sakandare". Shaidan ya kuma bayyana wa BBC cewar maharan sun harbi yaro ɗaya wanda aka garzaya da shi asibitin da ke garin Birnin Gwari. Yaran da lamarin ya rusta da su, kamar yadda shaidan ya tabbatar wa BBC shekarunsu sun kama ne daga takwas zuwa 15. Ya bayyana cewa an