Chelsea za ta yi nazari,kan makomar Pochettino, Flick zai koma Bayern Munich
GETTY IMAGES Bayanan hoto, Mauricio Pochettino Chelsea za ta yi nazarin karshen kakar wasa ta bana bayan wasan karshe na gasar Premier da za ta yi da Bournemouth , inda za ta yanke shawara kan makomar kocinta Mauricio Pochettino. (Telegraph) Arsenal na zawarcin tsohon mai tsaron ragar kungiyar da Poland Wojciech Szczesny, mai shekara 34, da golan Brighton Jason Steele dan Birtaniya da kuma na Ajax Diant Ramaj dan kasar Jamus yayin da su ke neman wanda zai maye gurbin Aaron Ramsdale, mai shekara 25 wanda zai bar Gunners. (Standard) Har illa yau Arsenal na kuma duba yiwuwar daukar golan Everton da Ingila Jordan Pickford, mai shekara 30 a wannan bazara. (Teamtalk) Gunners na kuma neman dan wasan baya da tsakiya da kuma mai kai hari a kokarin da suke yi domin fadada 'yan wasan kungiyar karkashin jagorancin Mikel Arteta. (Standard) Graham Potter ya ki amincewa da damar da aka bashi na zama kociyan Ajax, bayan da y...