Sojin Najeriya sun kashe jagoran 'yan fashin daji a jihar Sokoto
Copyright: Nigeria Army Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe wani jagoran 'yan fashin daji a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar. Wata sanarwa da ta fitar a shafukanta na intanet ta ce dakarun rundunar da aka tura don yaƙi da ta'addanci ne suka yi nasarar kashe jagoran, wanda ba ta bayyana sunansa ba, a ranar Laraba. "Bayan samun bayanan sirri, dakaru sun yi wa gungun 'yanta'addan kwanton-ɓauna a wata mashiga da ke ƙauyen Sarma a ƙaramar hukumar Tangaza, inda suka yi nasarar kashe jagoransu tare da ƙwato bindigar AK-47 da kuma babur," in ji sanarwar. A jihar Kaduna kuma, dakarun sojin sun yi nasarar katse hanzarin masu garkuwa da mutane a garin Kafanchan na ƙaramar hukumar Jema'a, sannan suka kama biyu daga cikinsu tare da ƙwato bindiga ɗaya, da harsasai, da kuma babur. Kazalika, wani ɗan fashi ya gamu da ajalinsa a wurin duba ababen hawa na Kaskara da ke ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato, lokacin da dakarun suka amsa kiran neman agaj...