Dalilin da ya sa majalisa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi
NingiASALIN HOTON, FB/NINGI Majalisar Dattijan Najeriya ta dakatar da sanata mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya, Sanata Abdul Ningi daga majalisar na tsawon wata uku bayan zargin shi da furta kalaman da ake ganin sun 'zubar da ƙimar majalisar.' A wani zama mai cike da hatsaniya, majalisar ta bai wa sanatocin damar yin bayani ɗaya bayan ɗaya, inda kusan dukkanin su suka nuna rashin jin daɗi kan kalaman sanata Ningi a wata tattaunawa da ya yi da sashen Hausa na BBC. Me sanata Ningi ya shaida wa BBC? Tattaunawar da Sanatan yayi a filin Gane Mini Hanya da sashen Hausa na BBC ke watsawa a rediyo duk ranar Asabar, ita ce ta tayar da ƙura a faɗin ƙasar, bayan da ya furta cewa akwai kasafin kuɗin ƙasar kala biyu da ake da su a yanzu haka. Ya ce "Bajet (budget) ɗin da aka yi, bayan wanda majalisa ta yi a fili an koma an yi wani bajet a ƙarƙashin ƙasa," Ya ƙara da cewa "abubuwan da muka gani sabbi ba mu taɓa jin labarinsu ba, amma har yanzu ƙwararru na fannin kuɗi da...