Matakai takwas da za ku bi don sayen shinkafar kwastam mai rahusa
Facebook/Nigeria Custome Copyright: Facebook/Nigeria Custome Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya kwastom ta fara sayar da shinkafa kan farashin mga 'yan kasar. Matakin na daga cikin ayyukan rage radadin tattalin arzikin da 'yan NAjeriya ke fuskanta Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Maiwada ya shaida wa BBC cewa shinkafar da hukumar ke sayarwa, shinkafa ce da jami'an hukumar suka kama a lokacin da aka shigar da ita kasar ba bisa ka'ida ba. Ya ce hukumar ta kai shinkafar kotu inda suka samu sahalewar kotu domin sayar da ita ga talakawan kasar. Abdullahi Maiwada ya ce an fara sayar da sayar da shinfara ne a yau Juma'a a jihar Legas, a matsayin gwaji kafin daga baya hukumar ta fadada aikin zuwa sauran jihohin kasar da take da irin wadannan kaya da ta kama. Kakakin hukumar ya ce suna sayar da buhu mai nauyin kilogiram 25 na shinkafar a kan kudi naira 10,000. Matakan da hukumar ke bi wajen sayar da shinkafar Abdullahi Maiwada ya ce hukumar na bin wasu mat...