Copyright: Nigerian Govt Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Festur Keyamo ya ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC na gudanar da bincike kan yarjejeniyar kamfanin jiragen sama na ƙasar wato 'Nagerian Air' mai cike da ce-ce-ku-ce da gwamnatin tarayya ta ƙulla ƙarƙashin tsohon ministan kula da sufurin jiragen sama na ƙasar Hadi Sirika Yayin da yake zantawa da gidan talbijin na Channels ranar Laraba, mista Keyamo ya ce “EFCC na bincike kan yarjejeniyar. ''Ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma muna jiran rahoton binciken''. Mista Keyamo wanda suka yi aiki tare da Siriki a matsayin ministocin gwamnatin Buhari, ya ce babu wani kamfanin jirage da ke aiki a matsayin kamfanin jirage na ƙasa, amma ya ce za a samar da nagartaccen kamfanin jirage na ƙasa. A watan Agustan bara ne Mista Keyamo ya ƙaryata yarjejeniyar da Sirika ya ƙulla tare da dakatar da duk wani shiri da ke cikin yarjejeniyar. Batun yarjejeniyar kamfanin 'Nigerian Air' da...