Posts

Showing posts from March 3, 2024

Ko kun san ƙwaƙular kunne na haifar da matsalar ji?

Image
Kunne wani ɓangare ne mai muhimmanci a jikin ɗan’adam wanda ya kamata a kula da shi. Kunnuwanmu na da mahimmanci ga lafiyarmu - amma duk da haka, galibi ba mu kula yadda ya kamata. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar uku ga watan Maris a matsayin "ranar ji ta duniya" don fadakar da al’umma muhimmancin kula da jinsu. Taken bikin ranar ta bana shi ne “sauya tunanin mutane game da matsalar ji” - domin an gano akwai wani tunanin da mutane suke da shi wanda ke kara haifar da matsala ga jinsu. Wata kididdiga ta Hukumar lafiya ta duniya ta nuna cewa aƙalla mutum miliyan 430 ne a fadin duniya ke fama da matsalar da ta shafi rashin ji, inda kuma a Najeriya fiye da mutum miliyan 20 ke fama da wannan matsalar. Alƙalumman sun nuna cewa yawan mutanen da ke da matsalar ji a duniya yana karuwa kusan kullum. Kuma masana sun ce galibi mutane ne ke yi wa kunnuwansu illa ba tare da sun sani ba ta hanyar bin wasu hanyoyi da ba su dace ba musamman ƙoƙarin cire dattin kunne ko idan sun ji sauyi ...