Posts

Showing posts from April 19, 2024

Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ruwa a jallo

Image
Bayanan hoto, Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello Ministan shari'ar Najeriya ya bayyana takaici kan yadda ya ce wasu 'yan siyasa ke kange kansu daga kamu bisa wasu laifuka da ake zargin sun aikata. Chief Lateef Olasunkanmi Fagbemi (SAN) ya bayyana hakan ne biyo bayan kulli-kurciyar da aka yi tsakanin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da jami'an hukumar EFCC inda a 'karshe suka kasa damke shi sakamakon kange shi da ake zargin wani jami'in gwammnati ya yi. Al'amarin ya sanya Minstan shari'a ya gargadi jami'an gwamnati wadanda dokar 'kasa ke karewa su guji kawo cikas a kokarin da ya cancanci yabo da hukumar EFCC ke yi. Mai sharhi, Barrister Audu Bulama Bukarti ya bayyana cewar akwai bukatar wannan gargadi abu ne da ya zama wajibi. '' Ita hukumar EFCC, hukuma ce da dokar Najeriya ta kafa ta kuma ba ta ikon ta binciki wanda ake zargi da laifi kuma wanda ake zargi da laifin komai girmansa a 'kasar''. Barrista Bulama ya kuma kar