Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ruwa a jallo
Ministan shari'ar Najeriya ya bayyana takaici kan yadda ya ce wasu 'yan siyasa ke kange kansu daga kamu bisa wasu laifuka da ake zargin sun aikata.
Chief Lateef Olasunkanmi Fagbemi (SAN) ya bayyana hakan ne biyo bayan kulli-kurciyar da aka yi tsakanin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da jami'an hukumar EFCC inda a 'karshe suka kasa damke shi sakamakon kange shi da ake zargin wani jami'in gwammnati ya yi.
Al'amarin ya sanya Minstan shari'a ya gargadi jami'an gwamnati wadanda dokar 'kasa ke karewa su guji kawo cikas a kokarin da ya cancanci yabo da hukumar EFCC ke yi.
Mai sharhi, Barrister Audu Bulama Bukarti ya bayyana cewar akwai bukatar wannan gargadi abu ne da ya zama wajibi. '' Ita hukumar EFCC, hukuma ce da dokar Najeriya ta kafa ta kuma ba ta ikon ta binciki wanda ake zargi da laifi kuma wanda ake zargi da laifin komai girmansa a 'kasar''.
Barrista Bulama ya kuma kara da cewa a dokokin Najeriya, kokarin kange wanda hukuma take nema babban laifi ne da doka ta tanadar wa da hukuncin zaman gidan kurkuku na shekara biyar ba tare da zabin tara ba.
Sannan za kuma a iya daure mutum kuma a ci tararsa idan har ya hana wata hukumar gwamnati ta yi bincike ko kuma ta kama wani da ake zargi ta hanyar kange shi ko boye shi ko kuma bayar da bayanan karya cewar ba ya guri bayan kuma yana gaurin.
Dacewar gargadin Ministan Shari'a
Awwal Musa Rafsanjani Shugaban Kungiyar Yaki da Cin Hanci da Karbar Rashawa ta Transparency International a Najeriya kuma darektan cibiyar CISLAC a kasar yana ganin wannan gargadi ya dace:
''In har za a yi wa wasu, wasu kuma ba za a yi musu ba, to akwai matsala, kamata ya yi a ce duk wadanda ake zargin sun yi irin wannan sace-sace ko rashin gaskiya to kar su kauce wa doka kar kuma su kauce wa binciken hukumar EFCC''.
Tun bayan da tsohon gwamnan jihar Kogin Yahaya Bello ya sauka daga mulki ake zargin yana samun kariya daga wanda ya gada daga kamun Hukumar EFCC.
Comments