Kotu ta tura Murja Kunya zuwa asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa
Wata kotu da ke zaman ta a birnin Kano ta bayar da umarnin tura ƴar tiktok Murja Ibrahim Kunya zuwa asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiyar ƙaƙwalwarta. Mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Babajibo Ibrahim ne ya tabbatar wa BBC hakan bayan zaman kotun da aka yi a yau Talata. A hirar sa da BBC, Babjibo ya ce "yanayin da take ciki da kamannunta da kuma maganganun da take faɗa sun nuna cewa ba ta cikin hali na cikakken hankali." Ya ƙara da cewa "wannan ne dalilin da ya sa alƙalin ya buƙaci a tura wadda ake zargin zuwa asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa har zuwa ranar 20 ga watan biyar, 2024." Hukumar Hizba ta jihar Kano ce ta kama Murja Kunya tare da miƙa ta ga jami'an tsaro bisa zargin ta da laifukan da suka shafi baɗala a shafukan sada zumunta. Kwamandan hukumar ta Hizba a jihar, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce tuhume-tuhumen da ake yi wa Murja Kunya sun haɗa da: Razana al'umma, ayyukan baɗala, tayar da hatsaniya, tayar da hankali...