Kotu ta tura Murja Kunya zuwa asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa

Murja Ibrahim Kunya

Wata kotu da ke zaman ta a birnin Kano ta bayar da umarnin tura ƴar tiktok Murja Ibrahim Kunya zuwa asibitin masu taɓin hankali domin duba lafiyar ƙaƙwalwarta.

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Babajibo Ibrahim ne ya tabbatar wa BBC hakan bayan zaman kotun da aka yi a yau Talata.

A hirar sa da BBC, Babjibo ya ce "yanayin da take ciki da kamannunta da kuma maganganun da take faɗa sun nuna cewa ba ta cikin hali na cikakken hankali."

Ya ƙara da cewa "wannan ne dalilin da ya sa alƙalin ya buƙaci a tura wadda ake zargin zuwa asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa har zuwa ranar 20 ga watan biyar, 2024."

Hukumar Hizba ta jihar Kano ce ta kama Murja Kunya tare da miƙa ta ga jami'an tsaro bisa zargin ta da laifukan da suka shafi baɗala a shafukan sada zumunta.

Kwamandan hukumar ta Hizba a jihar, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce tuhume-tuhumen da ake yi wa Murja Kunya sun haɗa da: Razana al'umma, ayyukan baɗala, tayar da hatsaniya, tayar da hankalin al'umma, kawo ɓata-gari cikin unguwa da kuma iƙirarin cewa ita ce shugaban karuwai da ƴan kwalta.

Batun kamawa da tura fitacciyar ƴar tiktok ɗin zuwa gidan yari ya ja hankalin al'ummar a jihar ta Kano.

Haka nan labarin fitar da ita daga inda kotu ta tura ta, wato gidan gyaran hali shi ma ya janyo muhawara mai zafi a jihar.

A ranar Litinin gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba ta da hannu a sakin ƴar tiktok ɗin daga gidan yari bayan umarnin da kotu ta bayar na tsare ta.

    Comments

    Popular posts from this blog

    An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

    Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

    Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano