Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga a Neja da Borno
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakarunta sun samu nasarar kashe 'yan bindiga da dama a jihohin Borno da Neja.
Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojin saman ƙasar, Edward Gabkwet ya ce cikin jerin wasu hare-hare ta sama da dakarun rundonin Hadin Kai da Whirl Punch suka ƙaddamar a jihohin biyu ya samu narasar lalata wasu shirye-shiryen 'yan bindigar.
Edward Gabkwet ya ce a ranar 3 ga watan Mayu dakarun ƙasar sun kai hari a garin Chinene da ke yankin tsaunin Mandara da ke kusa da jihar Borno.
Ya ce dakarun sojin ƙasar sun ga 'yan bindigar na wani taro da ake kyautata zaton tattaunawa suke yi a lokacin da jirgin sojin ya kai musu hari tare da kashe su.
“Haka kuma a garin sojojinmu sun hangi wasu motocin yaƙi bakwai da ake zaton na 'yan bindigar ne a ƙarƙashin wata bishiya, nan take su ma aka kai musu hari tare da lalata su'', in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa “bayanan da muka samu bayan hare-haren sun nuna cewa an samu nasara, domin kuwa hare-haren sun halaka 'yan bindigar da damarsu tare da lalata kayayyakinsu.''
Haka kuma sojojin sun ce sun kuma samu nasarar kai hari a ƙauyen Allawa da ke kusa da Shiroro a jihar Neja, inda aka kashe 'yan bindiga masu yawa.
Gabkwet ya ce sojojin sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri kan ƙaura da 'yan bindigar ke yi zuwa ƙauyen, lamarin da ya tilasta wa mazauna ƙauyen da dama tururuwar ficewa daga yankin sakamakon fargabar da suke yi.
Comments