Posts

Showing posts from March 1, 2024

Daurawa ya sauka daga shugabancin hukumar Hisbah a Kano

Image
1 Maris 2024, 06:44 GMT Wanda aka sabunta Mintuna 33 da suka wuce Fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi murabus daga muƙaminsa na shugaban hukumar Hisbah a Kano. Murabus ɗin malamin na zuwa kwana guda bayan da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna damuwarsa kan salon da hukumar Hisbah ke bi wajen yaƙi da masu aikata baɗala a jihar. A wani bidiyo mai tsawo ƙasa da minti uku da Sheikh Daurawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya bayyana cewa kalaman gwamnan sun kashe masa gwiwa kuma a don haka ya ajiye muƙaminsa na jagora a hukumar ta Hisba. Daurawa ya ce "Mun yi iya kokarinmu domin yin abin da ya kamata, to amma ina baiwa mai girma gwamna hakuri bisa fushi da yayi da maganganu da ya fada.Kuma ina rokon yayi mani afuwa na sauka daga wannan mukami da ya bani na shugabancin Hisbah."