Dakarun Najeriya sun kuɓutar da mutane daga hannun masu garkuwa a Taraba b
Kanawa post news Rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar wasu jami'an tsaro, sun lalata wata maɓoyar masu garkuwa da mutane tare da kuɓutar da mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a yankin ƙaramar hukumar Yorro na jihar Taraba. Cikin wata sanarwa da mai riƙon muƙamin daraktan yaɗa labaran rundunar sojin Najeriya ta 6 da ke jihar, Laftanar Oni Olubodunde ya sanya wa hannu, ya ce sojojin sun ƙaddamar da yaƙi da 'yan bindigar ne tun da suka yawaita kai hare-hare a yankin ƙaramar hukumar. Ya ƙara da cewa dakarunsu sun yi gumurzu da masu garkuwar a tsaunukan Gampu da na Ban Yorro, bayan musayar wuta tsakanin ɓangarorin ne, sai 'yan bindigar suka arce inda suka bar mutum huɗu da suka yi garkuwa da su. Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin za su ci gaba da aiki a yankin har sai sun tabbatar da kuɓutar da sauran mutanen da ke hannun masu garkuwar.