Tinubu ya aike da ta'aziyyarsa kan rasuwar shugaban Namibiya


Bola Ahmed Tinubu/XCopyright: Bola Ahmed Tinubu/X

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga al'ummar Namibiya bisa rasuwar shugaban ƙasar Hage Geingob.


Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya ce ya kaɗu da jin labarin rasuwar mista Geingob, wanda ya bayyana da ɗan kishin gwagwarmayar tabbatar da dimokraɗiyya.


Shugaban na Najeriya ya kuma bayyana marigayin da jagoran tabbatar da jagoranci nagari, da bunƙasa tattalin arziki da ci gaba al'ummar Afirka.


Shugaba Tinubu ya ce marigayin ya rasu ne a daidai lokacin da nahiyar Afirka ke buƙatar jajirtattun shugabanni irinsa, waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen bunƙasa nahiyar ta ko wanne fannin ci gaba.


Daga ƙarshe shugaba Tinubu ya ce a madadin gwamnatinsa da al'ummar Najeriya suna miƙa saƙon ta'aziyyarsu ga ɗaukacin al'ummar Nambiya bisa wannan babban rashi da suka yi.


Hage Geingob: Shugaban Namibia ya rasu yana dan shekara 82


Article share tools




Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano