Enzo na son Barcelona, Chelsea da Utd da PSG na ribibin Frenkie de Jong
Sa'o'i 2 da suka wuce Ɗanwasan tsakiya na Argentina Enzo Fernandez, mai shekara 23, na son raba gari da Chelsea ya koma Barcelona duk da kwangilarsa sai 2032 za ta kawo ƙarshe a Stamford Bridge. (Sport - in Spanish) Bayern Munich ta saka ɗanwasan Fulham da Portugal Joao Palhinha, mai shekara 28, cikin jerin ƴanwasan tsakiya da take hari a bazara. (Bild) Liverpool na sa ido kan ɗanwasan Fulham da Ingila mai shekara 26 Tosin Adarabioyo. (90min) Liverpool kuma na son ɗauko ɗanwasan baya na Fulham da Amurka Antonee Robinson, mai shekara 26, domin maye gurbin Andy Robertson, mai shekara 29. (Fichajes - in Spanish) Ɗanwasan baya na Bournemouth Lloyd Kelly, mai shekara 25, na dab da zuwa Liverpool ko Tottenham, a yayin da AC Milan da Juventus da sauran ƙungiyoyin Jamus ke ribibin ɗanwasan na Ingila. (Football Insider) Barcelona ta tuntuɓi E...