Posts

Showing posts from May 22, 2024

Puskas Arena zai karbi wasan karshe a Champions League 2026

Image
  ASALIN H Sa'o'i 2 da suka wuce Za a buga wasan karshe a Champions League a 2026 a Budapest a filin da ake kira Puskas Arena, inji Uefa ranar Laraba, bayan tashi daga babban taron da ta gudanar a Dublin. Filin dake cin Æ´an kallo 67,215 shine wajen da tawagar Hungary ke buga wasanni, wanda ya karbi bakuncin wasa hudu a Euro 2020 da na karshe a Europa League tsakanin Sevilla da Roma. An É—age taron zabar filin da zai shirya wasan karshe a 2027 zuwa watan Satumba, bayan da Uefa ke son jin karin bayani kan shirin gyaran San Siro, inda AC Milan da Inter ke wasanni. Haka kuma Uefa ta sanar da cewar za a buga wasan karshe a Champions League na mata a 2026 a Norway, Ullevaal Stadion. Shi kuwa filin wasa na Besiktas Park a Turkiya, zai shirya karawar karshe a Europa League a 2026 da kuma Europa Conference League a 2027. Jamus za ta karbi bakuncin wasa biyu - Filin wasa na Frankfurk zai shirya wasan karshe a Europa League a 2027 da kuma Europa Conference League a 2026 a filin RB Leipzig ...

shi a ranar 8 ga watan Agusta, 2021, bayan

Image
  shi a ranar 8 ga watan Agusta, 2021, bayan ya maye gurbin Eshaq Jahangiri, wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban Æ™asar Hassan Rouhani na farko. A cikin watan Yulin 2010, Tarayyar Turai ta saka Mohamed Mokhber a cikin jerin sunayen jami'an gwamnati da ta kakaba wa takunkumi tare da zarginsa da hannu a "ayyukan makami mai linzami na nukiliya", kuma bayan shekaru biyu ya cire sunansa daga jerin. An kuma sanya shi a cikin jerin takunkumin da ma'aikatar baitulmali ta Amurka ta a watan Janairun 2021. Washington ta fada a cikin jerin sunayen cewa kwamitin "yana da ruwa da tsaki a kusan kowane bangare na tattalin arzikin Iran, ciki har da makamashi da sadarwa da kuma sabis na kudi." Ya kasance na kusa da shugaban Iran Ebrahim Raisi, kuma ya kasance mai bin diddigin batutuwan cikin gida da dama. Ya ziyarci Æ™asashe da dama tare da sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannoni daban-daban cikin shekaru biyu da suka gabata. Mokhbar ya kuma kasance babban jami...