Posts

Showing posts from February 13, 2024

Falasɗinawa sun shiga fargaba gabanin hare-haren Isra'ila ta ƙasa a birnin Rafah

Image
ASALIN HOTON, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK Sa'o'i 3 da suka wuce Wani likita Bafalasɗine a birnin Rafah ya ce mutane sun kaɗu sosai saboda fargabar sabbin hare-haren Isra'ila, ta ƙasa, waɗanda ta ƙaddamar a Rafah, ɗaya daga cikin manyan birnin kudancin Gaza. a jerin saƙonnin da ya aikewa BBC , Dr Ahmed Abuibaid ya ce hare-haren saman su ƙazance, kuma sun shafi kusan dukkan sassan birnin. Ya ce "Tambayar da ta fi yawo a zukatan mutane a halin yanzu ita ce ina zamu?" A makon jiya ne Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sanar da kutsawar dakarunsa Rafah ta ƙasa, yana mai cewa za su faɗaɗa hare-hare. Fiye da rabin jama'ar Gaza da yawansu ya miliyan biyu ne yanzu haka suke zaman hijira a birnin Rafah mai maƙwabta da kan iyakar ƙasar Masar, duk da cewa mutane dubu 250 ne kacal ke rayuwa a birnin kafin ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas, a cikin watan Oktoban bara. Mafi yawan mutanen su na zaune ne cikin mawuyacin hali na rashin muhalli da...