Falasɗinawa sun shiga fargaba gabanin hare-haren Isra'ila ta ƙasa a birnin Rafah
Wani likita Bafalasɗine a birnin Rafah ya ce mutane sun kaɗu sosai saboda fargabar sabbin hare-haren Isra'ila, ta ƙasa, waɗanda ta ƙaddamar a Rafah, ɗaya daga cikin manyan birnin kudancin Gaza.
a jerin saƙonnin da ya aikewa BBC , Dr Ahmed Abuibaid ya ce hare-haren saman su ƙazance, kuma sun shafi kusan dukkan sassan birnin.
Ya ce "Tambayar da ta fi yawo a zukatan mutane a halin yanzu ita ce ina zamu?"
A makon jiya ne Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sanar da kutsawar dakarunsa Rafah ta ƙasa, yana mai cewa za su faɗaɗa hare-hare.
Fiye da rabin jama'ar Gaza da yawansu ya miliyan biyu ne yanzu haka suke zaman hijira a birnin Rafah mai maƙwabta da kan iyakar ƙasar Masar, duk da cewa mutane dubu 250 ne kacal ke rayuwa a birnin kafin ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas, a cikin watan Oktoban bara.
Mafi yawan mutanen su na zaune ne cikin mawuyacin hali na rashin muhalli da ruwan sha mai tsafta.
Shugaban hukumar kare ƴancin ɗan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk ya yi gargaɗi game da kai hari a yankin ba tare da bayar da kariya ga fararen huka ba.
Ya ce: "Akwai takaici ƙwarai da gaske, yadda ake kisan mata da ƙananan yara, da kuma raunata wasu da dama".
Haka nan kuma, Shugaba Biden na Amurka ya nemi a bayar da kulawar da ta dace ga Falasɗinawa fiye da miliyan ɗaya da ke neman mafaka a Rafah.
Da yake jawabi a fadar White House, Mr Biden ya ƙara jadadada buƙatar Isra’ila ta kiyaye kai hari Kudancin Gaza ba tare da ta yi tanadin kare fararen hula ba.
Ya ce "Mafi yawan waɗanda ke zaune a wajen, mutane ne da yaƙi ya ɗaiɗaita a lokuta da dama. Su na neman tsallakewa zuwa Arewaci, amma yaƙin ya ritsa da su, har suke neman mafaka a Rafah. Kuma tun daga furka mun riga mun sanar da matsayar mu, ba mu goyon bayan duk wani yunƙuri na fatattakar Falasɗinawa daga Gaza."
Comments