An buɗe wuraren ajiye kayan abinci da aka kulle a Kano
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano, ce ta buɗe manya-manyan wuraren ajiya da ta kulle a baya bisa zargin an ɓoye kayan abinci. Hukumar ta ce ta tattauna da masu wuraren inda suka cimma matsaya a kan yadda farashi zai sauka. A ƙarshen mako ne hukumar ta a'Anti-corruption' ta kai samame manyan rumbunan ajiye kayan abinci da ake zargin an boye kayan abinci a sassan jihar Kano bayan ƙorafe-ƙorafen da suka ce sun karɓa daga jama’a. Shugaban hukumar Muhyi magaji Rimin Gado, yace bayan sun garƙame rumbunan ajiye kayan abinci a wurare daban-daban ciki har da kasuwar Dawanau a Kano, masu wuraren sun kai kansu hukumar inda suka zauna tare da cimma matsaya. Kawo yanzu dai an buɗe manyan rumbunan ajiya da dama bayan zaman da aka yi. Shugabannin kasuwannin jihar sun tabbatar wa da BBC buɗe manyan rumbunan ajiyar. Shugaban hukumar anti-corruption mai yaki da cin hanci a Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado yace ko yanzu sun cimma manu...