Posts

Showing posts from April 23, 2024
Image
Copyright: Getty Images Kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki ya gayyaci ministan lantarki a Najeriya, Adebayo Adelabu da hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasar NERC da su bayyana gabansa a wani zaman bincike da za a yi game da ƙarin kuɗin lantarkin da aka yi a baya-bayan nan. Shugaban kwamitin majalisar, Sanata Enyinnaya Abaribe ne ya bayyana haka yayin gudanar da ayyukan kwamitin da kuma kai ziyara zuwa ma'aikatar lantarki da ke Abuja. Abaribe ya ce majalisar dattawa tuni ta amince a yi zaman ranar 29 ga watan Afrilu inda hukumomin gwamnati za su amsa tambayoyi. Ministan ya bayyana tarin matsalolin da suka addabi ɓangaren lantarki a Najeriya da suka haɗa da rashin isassun kuɗi da rashin iskar gas inda ya buƙaci kwamitin da ya tallafa wa ma'aikatar lantarki domin cimma ƙudurorinta. Kwamitin majalisar ya kuma duba wani aikin samar da wuta a harabar ma'aikatar. Sanata Abaribe ya kuma bayyana damuwa kan duk da maƙudan kuɗin da ake zubawa a ɓangaren lantarki, masu ruw