Posts

Showing posts from February 5, 2024

Tsohon Gwamnan Jihar Yobe Bukar Abba ya rasu

Image
ate Gv Copyright: Yobe State Gov Gwamnatin Jihar Yobe ta sanar da mutuwar tsohon Gwamnan jihar Sanata Bukar Abba Ibrahim. Cikin wata sanarwa da Gwamna Mai Mala Buni ya fitar ta hannun daraktan yaɗa labaransa Mamman Mohammed, ta ce ya mutu ne a Saudiyya bayan wata doguwar lafiya da ya yi fama da ita, sannan kuma za a binne shi a can. Gwamna Mai Mala ya yi umarnin a gudanar da zaman makoki kamar yadda aka saba a al'adance kuma gwamnati ce za ta gudanar da hakan ga marigayin. Mai Mala ne zai ci gaba da karɓar ta'aziyyar marigayin a masallacin gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu. Gwamna Bini ya bayyana mutuwar a matsayin gagarumin rashi ga gwamnati da kuma mutanen jihar. "Wannan ba ƙaramin rashi ba ne muka yi, amma haka Allah ya so, shi nemahaliccinmu, muna fatan ya yi masa gafara," in ji sanarwar. Marigayi Bukar Abba wanda ya wakilci Yobe ta Gabas a matsayin Sanata, ya mutu yana da sheka75.