Ana shirin mayar da wasu ofisoshin NUPRC zuwa Legas'
@NUPRCofficial/X Copyright: @NUPRCofficial/X Hukumar NUPRC mai sa ido kan harkokin man fetur a cikin ruwa a Najeriya ta kammala shirye-shiryen sauya matsugunnin wasu ofisoshinta daga Abuja zuwa Legas. Wannan da alama na zuwa ne bayan matakin baya-bayan nan na mayar da wasu ma'aikatan babban bankin Najeriya, CBN da sauya matsugunin hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya - FAAN da wani sashe na babban bankin kasar, CBN. Wasu ma'aikatan NUPRC sun tabbatar wa BBC cewa hukumar na shirye-shiryen ɗaukan wannan matakin. Matakin na mayar da wasu ma'aikatan CBN zuwa Legas da ɗauke hukumar FAAN zuwa BIRNIN ya janyo cece-kuce inda masu ruwa da tsaki suka nuna rashin gamsuwarsu da matakin. NUPRC da a baya ake kira DPR mai sa ido kan harkokin haƙowa da sayar da man fetur a Najeriya, sashe ne a ƙarƙashin ma'aikatar albarkatun man fetur ta Najeriya. Hukumar na lura da mai da iskar gas domin tabbatar da bin ƙa'idoji da dokokin da suka dace da kuma lura da was...