Kamfanin AEDC ya yi barazanar yanke wa fadar shugaban Najeriya wutar lantarki
PRESIDENCY NG Copyright: PRESIDENCY NG Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Image caption: Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja AEDC ya yi barazanar katse wutar lantarki a fadar shugaban Najeriya da na wasu ma’aikatun gwamnati 86 a kan bashin kuɗin wuta sama da naira biliyan 47 da yake bin su. Wasu daga cikin ma'aikatun da barazanar ta shafa sun haɗa da ma'aikatar kuɗi da ta yaɗa labarai da ta kasafin kuɗi da ta ayyuka da gidaje, da gwamnan CBN da ofishin Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da sauran su. A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Litinin, AEDC ɗin ya bai wa ma'aikatu da ofisoshin na gwamnati kwana 10 domin biyan basukan ko kuma a yanke musu lantarki, wato daga 28 ga watan Fabarairun 2024. Bangaren samar da wutar lantarki a Najeriya dai ya shafe shekaru yana fama da matsalar bashi. A makon da ya gabata ne Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da su t...