Kamfanin AEDC ya yi barazanar yanke wa fadar shugaban Najeriya wutar lantarki


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Image caption: Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja AEDC ya yi barazanar katse wutar lantarki a fadar shugaban Najeriya da na wasu ma’aikatun gwamnati 86 a kan bashin kuɗin wuta sama da naira biliyan 47 da yake bin su.

Wasu daga cikin ma'aikatun da barazanar ta shafa sun haɗa da ma'aikatar kuɗi da ta yaɗa labarai da ta kasafin kuɗi da ta ayyuka da gidaje, da gwamnan CBN da ofishin Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da sauran su.

A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Litinin, AEDC ɗin ya bai wa ma'aikatu da ofisoshin na gwamnati kwana 10 domin biyan basukan ko kuma a yanke musu lantarki, wato daga 28 ga watan Fabarairun 2024.

Bangaren samar da wutar lantarki a Najeriya dai ya shafe shekaru yana fama da matsalar bashi.

A makon da ya gabata ne Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da su tashi tsaye idan ba haka ba duk wanda aka samu da laifi, za a soke lasisin sa.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano