Za Mu Ɗauki Mataki Kan Duk Masu Sukar Shugaba Tinubu Kan Tattalin Arziƙi – Bello Matawalle




Ƙaramin Ministan Tsaron Nijeriya ya yi tsokaci kan koke-koken da jama’a ke yi kan matsin tattalin arziki da ƴan kasar ke fama da shi a yanzu haka.

Jaridar yanar gizo ta ‘Tarayya’ ta yi karin haske kan cewa, a cikin wannan shekarar, wasu fitattun ƴan Nijeriya, ciki har da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da shahrarren lauya Femi Falana sun bayyana rashin jin daɗinsu da halin da ƴan ƙasar suko

A makon jiya kuma, ƴan Nijeriya sun yi zanga-zanga a jihohin Neja da Kano da kuma Legas kan matsin rayuwa da suke fuskanta.

Gwamnatin Bola Tinubu ta ce tana ƙoƙarin warware matsalar ta hanyar raba kayan abincin da ke rumbunan gwamnati, sannan ta ɗora laifin taɓarɓarewar tattalin arziki kan tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano