Barcelona ta sake yin tuntuɓe a La Liga
Barcelona ta kasa cin gajiyar sakamakon sauran wsasannin da suka gudana a gasar La Liga bayan da ta yi canjaras 0-0 da Athletic Bilbao wanda hakan ke nufin ta ci gaba da kasancewa a matsayi na uku a kan teburi. Yayin da Girona da ke matsayi na biyu ta sha kashi a hannun Mallorca, Barcelona ta samu damar ɗarewa kanta a teburi idan ta yi nasara, amma Bilbao ta tabbatar da hakan bai faru ba. Yayin da Barcelona ke shirin fafatawa da Napoli a wasan zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun Turai ranar 12 ga Maris, kocin Barcelona Xavi ya shiga tsaka-mai-wuya yayinda Frenkie de Jong da Pedri suka bar filin wasa da raunuka. Sakamakon wasan dai ba yi wa kowanne ɓangare daɗi ba inda Barcelona ta maƙale a matsayi na uku da tazarar maki takwas tsakaninta da Real Madrid. Ita kuma Athletic Bilbao da ke matsayi na biyar ta ƙara samun koma baya a yaƙin neman matsayi na huɗu a teburin gasar inda ta samu kanta da tazarar maki biyar tsakaninta da Atletico Madrid wadda ta doke Real Betis da ci 2-1.