Za mu tsaurara tsaro a rumbunan ajiye kayan abinci - NEMA


  1. Hukumar kai ɗaukin gaggawa ta Najeiya (Nema) ta ce za ta tsaurar tsaro a rumbunan ajiye kayan abincinta da kuma ofisoshinta da ke faɗin Najeriya domin kare su daga 'ɓata-gari’

    Hakan na zuwa ne bayan harin da aka kai kan wani daga cikin rumbunanta da ke Abuja, babban birnin ƙasar a ranar Lahadi.

    Wasu matasa ne ake zargin sun kai farmaki kan rumbun wanda ke unguwar Gwagwa da ke birnin na Abuja, inda suka yi awon-gaba da kayan abinci da kuma sauran abubuwan da aka taskace a rmbun.

    Wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun hukumar ta NEMA, Manzo Ezekiel, ta ce "Shugaban hukumar na ƙasa, Mustapha Ahmed ya bayar da umarnin a tsaurara tsaro a ofososhi da kuma rumbunan ajiye kayan hukumar a faɗin Najeriya domin kauce wa kutsawa cikin su."

    Najeriya dai na fama da matsi na tattalin arziƙi, inda mutane da dama ke kokawa kan rashin abinci da tsadar kayan masarufi.

    Kafin fasa rumbun ajiye abincin a Abuja, an samu rahotannin yadda mutane suka far wa motocin dakon kayan abinci tare da yin wawason abin da suke ɗauke da shi a wasu sassan ƙasar.

    Ko a makon da ya gabata kungiyar ƙwadago ta ƙasar (NLC) ta gudanar da wata zanga-zangar yini ɗaya a ƙasar domin matsa wa gwamnati lamba kan ta ɗauki matakan da suka dace wajen kawo sauƙi ga matsalar rayuwa da al'umma ke ciki.

    Gwamnatin ƙasar dai ta ce ta fito da tsarin raba kayan tallafi ga al'umma da kuma bai wa masu



Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano